Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban Yan Fulani a Jihar Kwara

Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban Yan Fulani a Jihar Kwara

- Wasu yan bindiga sun kutsa cikin gidan shugaban fulanin garin Lamba, sun harbe shi har lahira a jihar Kwara

- Rahotanni sun bayyana cewa sun shiga har ɗakin kwanansa, suka harbe shi a ƙirji, saida suka tabbatar ya mutu

- Hukumar yan sandan jihar ta tabbatar da kisan, amma tace a halin yanzun tana gudanar da bincike kan lamarin

Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun kashe shugaban Fulani, Alhaji Abdullahi Hardo Buruku, wanda akafi sani da, Alhaji Malam, a garin Lamba, ƙaramar hukumar Asa, jihar kwara, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Mun Fara Tattaunawa da Yan Bindigan da Suka Sace Ɗaliban Islamiyya, Gwamnatin Neja Tayi Ƙarin Haske

Wannan na zuwa ne mako biyu bayan wasu yan bindiga sun kashe wani mai neman muƙamin 'magaji' a garin Balla, karamar hukumar Asa, kamar yadda punch ta ruwaito.

Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban Yan Fulani a Jihar Kwara
Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban Yan Fulani a Jihar Kwara Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Da yake magana kan kisan, tsohon sakataren Miyetti Allah a Kwara, Alhaji AbdulAziz Muhammed, yace maharan sun kutsa gidan Alhaji Malam dake Lamba da tsakar dare.

Yace: "Sun shiga gidan, suka tafi kai tsaye zuwa ɗakin kwanan shi, suka harbe shi a ƙirji, saida suka tabbatar ya mutu kafin su tafi."

"A halin yanzu, bamu zargin kowa kuma bamu san inda yan bindigan suke ba. Mun gudanar da jana'izarsa kamar yadda musulunci ya tanada."

KARANTA ANAN: Yanzu-Yanzu: Mahaifiyar Ɗaya Daga Cikin Ɗaliban da Aka Sace a Islamiyya Ta Rigamu Gidan Gaskiya

Kakakin hukumar yan sandan jihar Kwara, Ajayi Okasanmi, ya tabbatar da faruwar lamarin, yace hukumar ta fara bincike kan kisan.

"Eh, dagaske ne mun samu rahoton an kashe shugaban Fulani a Lamba, a halin yanzun mun fara bincike kan lamarin."

A wani labarin kuma Sama da Yan Najeriya 10,000 Sun Kamu da Rashin Lafiya Bayan an Musu Rigakafin COVID19 Kashi Na Farko

Hukumar Lafiya a matakin farko NPHCDA ta bayyana cewa yan Najeriya sama da 10,000 ne suka sami matsala bayan yin rigakafin korona, kamar yadda premium times ta ruwaito.

Shugaban NPHCDA, Dr Faisal Shu'aib shine ya bayyana haka a babban birnin tarayya Abuja ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262