Rahoto: Sama da Yan Najeriya 10,000 Sun Kamu da Rashin Lafiya Bayan an Musu Rigakafin COVID19 Kashi Na Farko

Rahoto: Sama da Yan Najeriya 10,000 Sun Kamu da Rashin Lafiya Bayan an Musu Rigakafin COVID19 Kashi Na Farko

- Hukumar Lafiya a matakin farko NPHCDA ta bayyana cewa yan Najeriya sama da 10,000 ne suka sami matsala bayan yin rigakafin korona

- Shugaban NPHCDA, Dr Faisal Shu'aib shine ya bayyana haka a babban birnin tarayya Abuja ranar Talata

- Yace dukkan waɗanda suka samu alamun ciwo bayan allurar rigakafin sun warke

Dataktan hukumar lafiya a matakin farko (NPHCDA), Dr. Faisal Shu'aib, yace sama da mutum 10,000 na yan Najeriya sun kawo rahoton samun matsala bayan an musu allurar rigakafin COVID19 kashi na farko, kamar yadda premium times ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Bayan an Biya Miliyan N5m, Yan Bindiga Sun Buƙaci a Basu Burodi da Lemun Kwalba a Matsayin Fansa

Dr. Shuaib, wanda ya bayyana haka yayin da yake jawabi a wurin taron kwamitin COVID19 ranar Talata, yace matsalolin da ƴan Najeriya suka samu sun haɗa da, zazzaɓi, jin zafi, da kunburi a wurin da aka tsira musu allurar.

Rahoto: Sama da Yan Najeriya 10,000 Sun Kamu da Rashin Lafiya Bayan an Musu Rigakafin COVID19 Kashi Na Farko
Rahoto: Sama da Yan Najeriya 10,000 Sun Kamu da Rashin Lafiya Bayan an Musu Rigakafin COVID19 Kashi Na Farko Hoto: @Drfaisalshuaib
Asali: Twitter

Ya ƙara da cewa sun samu rahoton wasu sunji alamun ciwon kai, tsananin zafi, Zazzaɓi, jiri da kuma canjin yanayin jiki.

"Kimanin yan Najeriya 10,027 ne suka kawo rahoton jin alamu daban-daban bayan sun karɓi rigakafin tunda aka fara zuwa 30 ga watan Mayu." inji shi.

KARANTA ANAN: Gwamna Ya Sallami Ma’aikata 532 a Jiharsa, Yace Yanzun Aka Fara

Ya ƙara da cewa, a halin yanzun dukkan waɗannan mutanen sun warke daga dukkan matsalolin da suka samu.

Dr. Faisal yace, jihohi 5 dake kan gaba wajen samun waɗannan rahotannin sune: Cross Rivers 1,040, Kaduna 1,071, Lagos 795, Yobe 555, sai kuma Jihar Kebbi 525.

Yace zuwa yanzun an yiwa yan Najeriya 1,956,598 rigakafin COVID19 ta Astrazeneca karon farko a faɗin ƙasar nan.

A wani labari Hukumar Kwastan Zata Fara Horad da Jami’an Kwastan Na Ƙasashen Waje Kan Yaƙi da Yan Ta’adda, Inji Hameed Ali

Shugaban NCS, Hameed Ali, yayi alƙawarin cewa hukumar sa zata fara horad da jami'an kwastan na nahiyar Africa, kamar yadda punch ta ruwaito.

Mr. Ali yace za'a samar da wuri na musamman da zai ɗauki jami'ai da dama domin basu horo kan yaƙi da ta'addanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel