Yanzu-Yanzu: Mahaifiyar Ɗaya Daga Cikin Ɗaliban da Aka Sace a Islamiyya Ta Rigamu Gidan Gaskiya
- Ɗaya daga cikin iyayen ɗaliban islamiyyar jihar Neja da aka sace ɗalibanta ta rigamu gidan gaskiya
- Mahaifiyar ta yanke jiki ta faɗi lokacin da aka shaida mata labarin abinda ya faru na satar Yaran
- Shugaban makarantar, Alhaji Abubakar Alhassan, shine ya bayyana haka ranar Laraba
Ɗaya daga cikin iyayen ɗaliban da aka sace a makarantar islamiyyar Salihu Tanko a garin Tegina, ƙaramar hukumar Rafi jihar Neja ta mutu saboda takaici.
KARANTA ANAN: Rahoto: Sama da Yan Najeriya 10,000 Sun Kamu da Rashin Lafiya Bayan an Musu Rigakafin COVID19 Kashi Na Farko
Shugaban makarantar, Alhaji Abubakar Alhassan, shine ya bayyana haka ranar Laraba, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Yace mahaifiyar, wadda ta yanke jiki ta faɗi lokacin da aka faɗa mata an ɗauke ɗaliban, ta rasa rayuwarta daga baya a asibiti.
A wani saƙon murya dake yawo tsakanin jaridu, Alhassan Abubakar, yace yan bindigan sun tabbatar da mutum 150 suka ɗauke.
Alhassan yace: "Ɗaya daga cikin iyayen yaran da aka sace ta mutu saboda lokacin da aka faɗi mata ta yanke jiki ta faɗi, nan da nan aka kaita asibiti, amma daga baya aka bayyana rasuwarta."
Legit.ng hausa ta kawo muku rahoton cewa shugaban makarantar yayi magana da yan bindigan ta wayar salula.
KARANTA ANAN: Bayan an Biya Miliyan N5m, Yan Bindiga Sun Buƙaci a Basu Burodi da Lemun Kwalba a Matsayin Fansa
Yace ɗaya daga cikin malaman makarantar da aka sace yayi masa ƙorafin cewa yan bindigan sun fara bugun su, hara takai ga wasu yaran basa iya motsawa.
A wani labarin kuma Gwamna Ya Sallami Ma’aikata 532 a Jiharsa, Yace Yanzun Aka Fara
Gwamnan jihar Plateau, Simon Baƙo Lalong, ya sallami ma'aikata sama da 532 a jihar sa bayan ya gano akwai matsala a bayanan karatunsu.
Gwamnan yace ya ɗauki wannan matakin ne bayan gano ma'aikatan sun bada bayanan ƙarya, kamar yadda the nation ta ruwaito.
Asali: Legit.ng