Mun Fara Tattaunawa da Yan Bindigan da Suka Sace Ɗaliban Islamiyya, Gwamnatin Neja Tayi Ƙarin Haske

Mun Fara Tattaunawa da Yan Bindigan da Suka Sace Ɗaliban Islamiyya, Gwamnatin Neja Tayi Ƙarin Haske

- Gwamnatin jihar Neja ta bayyana cewa ta fara tattaunawa da yan bindigan da suka sace ɗaliban islamiyya a garin Tegina

- Gwamnatin ta tabbatar wa iyayen yaran cewa su kwantar da hankalinsu, yayan su zasu dawo gida lami lafiya

- Mataimakin gwamnan jihar, Muhammed Ketso, shine ya bayyana haka ga manema labarai a Minna

Gwamnatin jihar Neja ta bayyana cewa ta fara tattaunawar neman masalaha da yan bindigan da suka sace ɗaliban makarantar islamiyyar Salihu Tanko dake Tegina ƙaramar hukumar Rafi jihar Neja, kamar yadda daily Nigerian ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Yanzu-Yanzu: Mahaifiyar Ɗaya Daga Cikin Ɗaliban da Aka Sace a Islamiyya Ta Rigamu Gidan Gaskiya

Gwamnatin tace ta fahinci an fara tattauna wa tsakanin yan bindigan da iyayen yaran, amma tace ita ba zata biya ko sisi da sunan kuɗin fansa ba.

Mataimakin gwamnan jihar, Muhammad Ketso, shine ya bayyana haka a Minna Ranar Laraba yayin da yake zantawa da manema labarai, kamar yadda punch ta ruwaito.

Mun Fara Tattaunawa da Yan Bindigan da Suka Sace Ɗaliban Islamiyya, Gwamnatin Neja Tayi Ƙarin Haske
Mun Fara Tattaunawa da Yan Bindigan da Suka Sace Ɗaliban Islamiyya, Gwamnatin Neja Tayi Ƙarin Haske Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Yace: "Gwamnati ta fara tattaunawa da yan bindigan kan yadda za'a saki ɗaliban, kuma muna da tabbacin ba tare da jimawa ba yaran zasu gana da iyayen su."

"Gwamnati na tuntuɓar wasu daga cikin iyayen ɗaliban, kuma mun tabbatar musu da cewa ƴaƴansu zasu dawo cikin ƙoshin lafiya."

KARANTA ANAN: Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle Yayi Magana Kan Shirinsa Na Sauya Sheƙa Zuwa APC Ranar 12 Ga Yuni

Mataimakin gwamnan yace rahoton da ake yaɗawa cewa ɗalibai 200 aka sace ba gaskiya bane, su 163 ne aka sace harda malamai.

Mr. Ketso yace gwamnati ya hana amfani da mashinan yan kasuwa a faɗin garin Minna, kuma wannan dokar zata fara aiki ranar 3 ga watan Yuni.

A wani labarin kuma Bayan an Biya Miliyan N5m, Yan Bindiga Sun Buƙaci a Basu Burodi da Lemun Kwalba a Matsayin Fansa

Bayan an biyasu miliyan N5m, yan bindiga sun nemi a basu burodi da lemun kwalba mai sanyi a matsayin fansa.

Ɗan uwan matashin da aka sace, Mashood Adebayo, shine ya bayyana irin halin da suka shiga domin kuɓutar da ɗan uwansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel