Daliban Islamiyya: 'Yan Bindiga Sun Magantu, Sun Ba Da Wa'adin Biyan Kudin Fansa

Daliban Islamiyya: 'Yan Bindiga Sun Magantu, Sun Ba Da Wa'adin Biyan Kudin Fansa

- 'Yan bindigan da suka sace daliban makarantar Islamiyya sun bayyana kudin da suke bukata

- Sun kuma bayyana wa'adin da suke so a biya idan ba haka ba kuma su hallaka dukkan yaran

- Gwamnatin jihar ta ce ba za ta biya kudin fansa ba, kuma za ta yi kokarinta wajen ceto yaran

'Yan bindiga da suka sace daliban makarantar Salihu Tanko Islamiyya da ke garin Tegina a karamar hukumar Rafi ta jihar Neja sun tuntubi shugabannin makarantar.

'Yan bindigan sun tuntubi shugaban makarantar, Alhaji Abubakar Alhassan, da misalin karfe 4 na yamma a ranar Litinin, inda suka nemi ya biya N110m a matsayin kudin fansa don sakin daliban.

Da yake magana da manema labarai ta wayar tarho a ranar Talata, Alhassan ya ce 'yan bindigan sun yi ikirarin suna da yara 156 a hannunsu.

A cewarsa, masu garkuwar sun yi barazanar cewa idan ba su biya kudin fansar ba zuwa karshen yau (Laraba), za su kashe yaran duka.

KU KARANTA: Za Ku Shiga Firgici: Shugaba Buhari Ya Kalubalanci Masu Kitsa Kifar Da Gwamnatinsa

Sace Daliban Islamiyya: 'Yan Bindiga Sun Magantu, Sun Ba Da Wa'adin Biyan Kudin Fansa
Sace Daliban Islamiyya: 'Yan Bindiga Sun Magantu, Sun Ba Da Wa'adin Biyan Kudin Fansa Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Alhassan ya ce an mika sakon ga gwamnatin jihar, wacce ta ce ba za ta biya ko sisi ba.

Jaridar Punch ta gano cewa wasu masu kishin al'umma a cikin al'umma sun fara tara kudin.

A halin da ake ciki, gwamnatin jihar ta ce ta shirya kayan aiki da suke bukata don tabbatar da an sako yaran makarantar lafiya.

Wata sanarwa da Mary Noel Berje, Sakataren yada labarai na Gwamna Abubakar Bello, ta ruwaito Mataimakin Gwamnan Jihar, Alhaji Ahmed Ketso na cewa, “Gwamnati na kan farautar 'yan bindigan kuma ana kokarin gano su."

Hakazalika gwamnatin jihar bata tabbatar da adadin yaran da aka sace ba, amma ta shaidawa al'umma cewa tana iya kokarinta wajen ganin an sako yaran cikin koshin lafiya, Vanguard ta ruwaito.

“Ba a tabbatar da yawan yaran da aka sace ba. Duk da haka, kokarin da hukumomin tsaro ke yi don ganin an sake su ya tsananta. Ba za mu biya kudin fansa ga masu satar mutane ba. Muna kokarin tattaunawa domin ganin yadda za mu dawo da su lafiya.”

KU KARANTA: Rahoto: An Gargadi Ahmed Gulak Kada Ya Tafi Imo, Amma Ya Yi Biris

A wani labarin, Hukumomin tsaro a jihar Kaduna sun ba da rahoton wani mummunan hari da ‘yan bindiga suka kai wa al’ummar Goska a karamar hukumar Jema’a da ke jihar ta Kaduna, inda suka kashe mutum hudu.

Samuel Aruwan, Kwamishinan Ma’aikatar Tsaro na Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida, na Jihar Kaduna, ya fada a ranar Talata cewa ‘yan bindiga sun mamaye yankin suka kashe mutanen hudu.

“Wadanda aka kashen sunayensu; Wakili Kon, Yusuf Joshua, Martha Ayuba da Lami Peter," in ji shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel