Za Ku Shiga Firgici: Shugaba Buhari Ya Kalubalanci Masu Kitsa Kifar Da Gwamnatinsa

Za Ku Shiga Firgici: Shugaba Buhari Ya Kalubalanci Masu Kitsa Kifar Da Gwamnatinsa

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kalubalanci masu fafutukar kifar da gwamnatinsa

- Ya ce ya basu isassehen lokaci, kuma su sani nan kusa za su sha kunyar abubuwan da suke yi

- Shugaba Buhari na yin martani ne kan yawaitar hare-hare a kan kadarorin gwamnati da ake

Shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya ya bayyana fushinsa ga masu kitsa kifar da gwamnatinsa ta hanyar kai hare-hare kan kayayyaki mallakar gwamnati.

Ya ce duk masu wannan mummunan aiki su sani, yana sane kuma nan ba da dadewa ba za su sha kunyar abubuwan da suke aikatawa.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar ta shafin Tuwita, wanda Legit.ng Hausa ta gano a yau Talata 1 ga watan Yuni.

KU KARANTA: El-Rufai Ya Sake Sabbin Nadi a Gwamnatinsa, Ya Yi Garanbawul a Wasu Wurare

Za Ku Sha Kunya: Shugaba Buhari Ya Kalubalanci Maso Son Kifar Da Gwamnatinsa
Za Ku Sha Kunya: Shugaba Buhari Ya Kalubalanci Maso Son Kifar Da Gwamnatinsa Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Shugaban yace:

"Ina samun rahotannin tsaro na yau da kullun game da hare-haren da ake kaiwa a kan muhimman kayayyakin kasa, kuma a bayyane yake karara cewa wadanda ke bayan hare-haren suna son wannan gwamnatin ta kife ne.

"Duk wanda yake son lalata tsarin nan ba da dadewa ba zai gamu da firgici a rayuwarsa. Mun basu isasshen lokaci."

Najeriya na ci gaba da fuskantar hare-haren 'yan ta'adda a ofisoshin 'yan sanda da na hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC.

KU KARANTA: Rahoto: An Gargadi Ahmed Gulak Kada Ya Tafi Imo, Amma Ya Yi Biris

A wani labarin, Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa bata da kudirin nemn zarcewa kan mulki zango na uku kuma zai yi duk mai yuwuwa domin tabbatar da anyi zaɓe a 2023 duk kuwa da matsalar tsaron da ake fama da ita.

Shugaban ya bayyana haka ne a wani jerin rubutu da ya wallafa a shafinsa na tuwita @MBuhari bayan ganawa da shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu.

Legit.ng hausa ta nago cewa mako huɗu da suka wuce, an kai hari ofisoshin INEC 11, Inda ko dai a ƙona ofishin ko kuma a ruguza shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.