Tsageru Sun Kashe Shugaban Matasan PDP a Imo, Sun Kona Gidansa Da Motoci

Tsageru Sun Kashe Shugaban Matasan PDP a Imo, Sun Kona Gidansa Da Motoci

- Rahoto daga jihar Imo sun bayyana cewa, an hallaka shugaban matasa na jam'iyyar PDP

- An kuma ce an kone gidansa kurmus, tare da motocinsa da ke ajiye a cikin gidan a daren Litinin

- Hakazalika an hallaka wasu mutane biyu daga cikin danginsa dake tare dashi a cikin gidan

Wasu ‘yan bindiga, a ranar Talata, sun kashe shugaban matasa na jam’iyyar PDP na karamar hukumar Oru-East na jihar Imo, Kenneth Amukamara, jaridar Punch ta ruwaito.

'Yan bindigan sun kuma kona gidan Kenneth tare da lalata motocin dan uwansa, wanda aka ce soja ne mai ritaya.

Lamarin da ya faru a Umuokwe, Eziawo 1, a cikin karamar hukumar, ya kara tayar da hankali a yankin.

KU KARANTA: Za Ku Shiga Firgici: Shugaba Buhari Ya Kalubalanci Masu Kitsa Kifar Da Gwamnatinsa

Tsageru Sun Kashe Shugaban Matasan PDP Na Imo, Sun Kona Gidansa Da Motoci
Tsageru Sun Kashe Shugaban Matasan PDP Na Imo, Sun Kona Gidansa Da Motoci Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Wani dan jarida, Don Uba, wanda ya yi magana kan kisan shugaban matasan, ya ce mazauna yankin na cikin firgici.

Uba ya ce, “An kashe shugaban matasan jam’iyyar PDP a karamar hukumar Oru-East, Kenneth Amukamara da safiyar yau (Talata) a mahaifar kasarsa.

“Gidansa ma an cinna masa wuta. Kokarin da aka yi don tabbatar da mummunan lamarin daga bakin Shugaban Matasa na Jam’iyyar PDP na Jihar Imo, Greg Nwadike, wanda ya yi tattaki zuwa Abuja don wani aiki, abin ya ci tura har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

“Bayanai sun nuna cewa shi ma dan uwan nasa an yi kokarin kashe shi, amma ya samu damar tserewa kasancewar shi jami’in soja ne mai ritaya. Gidan Kenneth da motocinsa ba a bar su ba kamar yadda aka cinna musu wuta tare da lalata su.”

Shugaban matasan na PDP na jihar, Greg Nwadike, ya fada a cikin wata sanarwa a ranar Talata cewa baya ga kashe Kenneth, maharan sun kuma bankawa gidan mamacin wuta.

Nwadike ya ce jam’iyyar, musamman bangaren matasa, ta yi bakin ciki da kisan.

Sanarwar ta ce, “A karshe ina mai tabbatar da kisan Shugaban Matasan PDP na Karamar Hukumar Oru-East LGA, Jihar Imo, Kenneth Amukamara.

“Maharan sun kashe shi ne a daren Litinin a gidansa da ke Awo-Omamma kuma an ce an banka wa gidansa wuta.

“Bayanin da aka samu ya nuna cewa an kashe wasu 'yan uwansa biyu.

“Na sha yin gargadi ga matasan Imo da su guji fadawa cikin rikici kuma su zauna lafiya. Fatan Allah ya jikansa.”

Amma kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Bala Elkana, ya ce ba a kai rahoton faruwar lamarin ga 'yan sanda a jihar ba.

Lamarin tsaro na ci gaba da ta'azzara a yankin kudu maso gabashin Najeriya, lamarin da ya kai ga kashe-kashe da kone-konen mutane da kadarori mallakar gwamnati.

Rahotanni a bayan sun bayyana cewa, an kashe wani jigon jam'iyyar APC, Ahmed Gulak a jihar ta Imo, a yayin wata ziyara ta aiki da ya kai a jihar a makon da ya gabata.

KU KARANTA: Ba a Rubuta Kundin Tsarin Mulkin Najeriya Cikin Natsuwa Ba, Shugaban Majalisa

A wani labarin, Wani rahoto na musamman da jaridar The Cable ta fitar ta yi ikirarin cewa an gargadi Ahmed Gulak, sanannen jigo a jam’iyyar APC kan yin tafiya zuwa jihar Imo inda daga karshe aka harbe shi.

Jaridar, ta ambato wata majiya, da ta bayyana cewa Gulak ya yanke shawarar zuwa Owerri, babban birnin jihar Imo, domin jin ra’ayoyin jama’a game da sake duba kundin tsarin mulki, duk da gargadin da aka yi masa.

An ce marigayi dan siyasar ya dage kan tafiyarsa, yana mai cewa dukkanmu 'yan Najeriya ne.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel