NIN: Dubbannin Ɗalibai Ba Zasu Samu Damar Zana Jarabawar JAMB 2021 Ba, Inji NANS

NIN: Dubbannin Ɗalibai Ba Zasu Samu Damar Zana Jarabawar JAMB 2021 Ba, Inji NANS

- Ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa (NANS) reshen Kaduna ta nuna rashin jin daɗin ta kan matakin wajabta amfani da profile code wajen yin rijista

- Shugaban NANS na Kaduna, Huzaifa Bello, yace dubbannin ɗalibai ne zasu rasa damar yin jarabawar saboda rashin mallakar lambobin

- Yayi kira ga hukumar da ta sake duba yuwuwar ƙara wa'adin rijista ga ɗaliban da basu samu damar yi ba saboda wannan matsalar

Ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa (NANS) reshen jihar Kaduna ta nuna damuwarta ganin cewa dubbannin ɗalibai ka iya rasa damar zama jarabawar JAMB ta wannan shekarar saboda matsalolin da suke fuskanta da NIN/profile code, kamar yadda the nation ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Ba’a Taɓa Samun Gwamnati a Tarihin Najeriya da Tayi Ayyukan Cigaba Kamar Ta Buhari Ba, Lai Muhammed

Shugaban NANS na jihar Kaduna, Huzaifa Bello, a wani jawabi da ya fitar, ya nuna rashin amincewarsa da matakin da hukumar JAMB ta ɗauka.

NIN: Dubbannin Ɗalibai Ba Zasu Samu Damar Zana Jarabawar JAMB 2021 Ba, Inji NANS
NIN: Dubbannin Ɗalibai Ba Zasu Samu Damar Zana Jarabawar JAMB 2021 Ba, Inji NANS Hoto: sunnewsonline.com
Asali: UGC

Saboda haka shugaban yayi kira ga hukumar da ta ƙara wa ɗaliban dake son yin rijista lokaci kafin ta rufe damar rijistar jarabawar ta bana.

Maimakon Matakin da hukumar ta ɗauka na cewa duk ɗalibin da ya samu matsalar yaje hedkwatar JAMB ta jiharsa su masa rijista.

KARANTA ANAN: Da Dumi-Ɗumi: Buhari Ya Nemi Majalisa Ta Tabbatar da Nadin Sabon COAS, Manjo Janar Yahaya

Mr. Bello yace: "JAMB ta jawo dubbannin ɗalibai ba su yi rijista ba saboda sun kasa samun profile code kafin wa'adin 27 ga watan Mayu da hukumar ta saka ya cika."

"Mun samu kiraye-kiraye daga ɗalibai da iyayen yara waɗanda suka nuna rashin jin daɗin su akan matakin da JAMB ta ɗauka na wajabta amfani da profile code kafin yin rijista."

"Daga ƙididdigar da muka samu, hukumar tayi rijistar dalibai 1.3 miliyan ne kacal yayin da a shekarar data gabata ta samu dalibai miliyan biyu."

Bello yayi kira ga hukumar shirya jarabawar JAMB da ta sake ƙara sati biyu domin baiwa wasu ɗalibai daman yin rijista.

A wani labarin kuma Gwamna Matawalle Ya Dakatar da Sarki, Hakimi Bisa Zargin Taimaka Wa Yan Bindiga, Ya Naɗa Kwamitin Bincike

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya dakatad da Sarkin Ɗansadau, Hussaini Umar, da hakimin Nasarawa Mailayi, Bello Wakkala, bisa zarginsu da hannu a ayyukan yan bindiga.

A cewar jawabin da mai taimaka wa gwam nan kan yaɗa labarai, Zailani Baffa, ya fitar yace dakatarwar zata fara aiki nan take, kamar yadda daily Nigerian ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: