Bayan an Biya Miliyan N5m, Yan Bindiga Sun Buƙaci a Basu Burodi da Lemun Kwalba a Matsayin Fansa

Bayan an Biya Miliyan N5m, Yan Bindiga Sun Buƙaci a Basu Burodi da Lemun Kwalba a Matsayin Fansa

- Bayan an biyasu miliyan N5m, yan bindiga sun nemi a basu burodi da lemun kwalba mai sanyi a matsayin fansa

- Ɗan uwan matashin da aka sace, Mashood Adebayo, shine ya bayyana irin halin da suka shiga domin kuɓutar da ɗan uwansu

- Wasu yan bindigan sun sace wani matashi a Ilorin jihar Kwara yayin da ya fita domin dubo gonar sa

Wasu yan bindiga da suka sace Muritala Adebayo a Ilorin jihar Kwara sun buƙaci a basu burodi da lemun kwalba bayan sun amshi kuɗi miliyan N5m, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Bamu da Kudirin Zarcewa a Kan Mulki, INEC Zata Gudanar da Zaɓen 2023, Shugaba Buhari

Ɗan uwan wanda aka sace, Moshood Adebayo, ya bayyana halin da iyalan gidansu suka shiga a ƙoƙarin kuɓutar da ɗan uwansu.

Bayan an Biya Miliyan N5m, Yan Bindiga Sun Buƙaci a Basu Burodi da Lemun Kwalba a Matsayin Fansa
Bayan an Biya Miliyan N5m, Yan Bindiga Sun Buƙaci a Basu Burodi da Lemun Kwalba a Matsayin Fansa Hoto: dailytrust.com

Yace da farko yan bindigan sun nemi a biya miliyan N100m kuɗin fansa amma daga baya suka amince a basu 5 miliyan.

Yace : "Sun kirani da misalin ƙarfe 11:00 na dare ranar Litinin, suka umarce ni inzo Okolowo da miliyan N5m, tare da lemun coca-cola mai sanyi guda uku, da burodi guda biyar."

"Sun umarce ni in aje kayan tare da kuɗin a kan wata hanya da zata kaini garin Jabba daga Shao."

KARANTA ANAN: Babbar Magana: Dubbannin Ɗalibai Ka Iya Rasa Damar Zana Jarabawar JAMB 2021, Inji NANS

Legit.ng hausa ta gano cewa yan bindigan sun sace Muritala ne a Pampo dake ƙaramar hukumar Ala jihar Kwara yayin da ya fita duba gonarsa.

Muritala dai ya fito ne daga Ile Olosan (Shagaya) yankin Apomu dake Ilorin, babban birnin jihar Kwara.

A wani labarin kuma Ba’a Taɓa Samun Gwamnati a Tarihin Najeriya da Tayi Ayyukan Cigaba Kamar Ta Buhari Ba, Lai Muhammed

Ministan yaɗa labarai, Lai Muhammed, yace ayyukan cigaban da gwamnatin Buhari Tayi zasu amfanar da mutane da dama nan gaba, kamar yadda DailyNigerian ta ruwaito.

Ministan yace ba a taɓa samun wata gwamnati ba da ta samu nasarori ba kaɗan ɗin da take samu kamar wannan gwamnatin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel