Bamu da Kudirin Zarcewa a Kan Mulki, INEC Zata Gudanar da Zaɓen 2023, Shugaba Buhari

Bamu da Kudirin Zarcewa a Kan Mulki, INEC Zata Gudanar da Zaɓen 2023, Shugaba Buhari

- Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa gwamnatinsa bata sha'awar zarcewa akan mulki

- Buhari yace zai yi duk me yuwuwa wajen ganin an gudanar da zaɓe a 2023 duk da matsalar tsaron da ƙasar ke ciki

- Buhari ya faɗi haka ne a shafinsa na kafar sada zumunta bayan ganawa da shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa bata da kudirin neman zarcewa kan mulki zango na uku kuma zai yi duk mai yuwuwa domin tabbatar da anyi zaɓe a 2023 duk kuwa da matsalar tsaron da ake fama da ita.

KARANTA ANAN: Babbar Magana: Dubbannin Ɗalibai Ka Iya Rasa Damar Zana Jarabawar JAMB 2021, Inji NANS

Shugaban ya bayyana haka ne a wani jerin rubutu da ya wallafa a shafinsa na tuwita @MBuhari bayan ganawa da shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu.

Bamu da Kudirin Zarcewa a Kan Mulki, INEC Zata Gudanar da Zaɓen 2023, Shugaba Buhari
Bamu da Kudirin Zarcewa a Kan Mulki, INEC Zata Gudanar da Zaɓen 2023, Shugaba Buhari Hoto: @channelstv
Asali: Twitter

Legit.ng hausa ta nago cewa mako huɗu da suka wuce, an kai hari ofisoshin INEC 11, Inda ko dai a ƙona ofishin ko kuma a ruguza shi.

KARANTA ANAN: Ba’a Taɓa Samun Gwamnati a Tarihin Najeriya da Tayi Ayyukan Cigaba Kamar Ta Buhari Ba, Lai Muhammed

Wani ɓangaren rubutun shugaba Buhari yace:

"Na samu rahoto yau daga bakin shugaban INEC a kan jerin hare-haren da ake kaiwa kayayyakin hukumar a faɗin ƙasar nan."

"Ba zamu amince da waɗannan hare-haren ba, kuma ba zamu bar masu hannu a lamarin su cimma buƙatun su ba."

"Na tabbatar wa INEC zamu basu duk abinda suke buƙata, saboda kada wani ya sake cewa bamu son sauka daga kan mulki ko muna son zarcewa zango na uku. Babu dalilin da zamu gaza, zamu samar wa INEC duk abinda ta buƙata."

A wani labarin kuma Buhari Ya Nemi Majalisa Ta Tabbatar da Nadin Sabon COAS, Manjo Janar Yahaya

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya nemi majalisar dattijai data tabbatar da sabon shugaban rundunar sojin ƙasa, Mejo Janar Farouk Yahaya.

Shugaban majalisar, sanata Ahmad Lawan, shine ya karanta wasiƙar shugaban a zamanta na yau Talata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel