Da Ɗuminsa: IPOB Sun Sake Kai Sabon Hari Caji Ofis, Yan Sanda Sun Sheƙe 4 Daga Cikinsu

Da Ɗuminsa: IPOB Sun Sake Kai Sabon Hari Caji Ofis, Yan Sanda Sun Sheƙe 4 Daga Cikinsu

- Wasu yan bindiga da ake kyautata zaton yan IPOB ne sun sake kai sabon hari caji ofis ɗin yan sanda a jihar Imo

- Kakakin rundunar yan sandan jihar, Bala Elkana, shine ya tabbatar da haka, yace jami'an dake bakin aiki sun kashe huɗu daga cikinsu

- A halin yanzu, jami'an yan sanda na cigaba da bincike da nufin gano inda ragowar maharan suke, kuma a kamo su

Wasu yan bindiga da ake tsammanin mayaƙan IPOB ne sun kai hari ofishin yan sanda dake Izombe ƙaramar hukumar Ogunta jihar Imo, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamna Ya Hana Amfani da Babur, Keke Nafef a Faɗin Jiharsa

Wannan na zuwa ne awanni 24 bayan wasu yan bindiga sun kai hari caji ofis ɗin yan sanda dake Atta ƙaramar hukumar Najba jihar ta Imo, kmar yadda punch ta ruwaito.

Da Ɗuminsa: IPOB Sun Sake Kai Sabon Hari Caji Ofis, Yan Sanda Sun Sheƙe 4 Daga Cikinsu
Da Ɗuminsa: IPOB Sun Sake Kai Sabon Hari Caji Ofis, Yan Sanda Sun Sheƙe 4 Daga Cikinsu Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Rahoto ya nuna cewa huɗu daga cikin maharan sun rigamu gidan gaskiya a yayin musayar wutar da suka yi da jami'an dake bakin aiki.

Kakakin yan sandan jihar Imo, Bala Elkana, yace an kai sabon harin da misalin ƙarfe 7:00 zuwa 10:00 na daren ranar Asabar.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Sojoji Sun Fatattaki Harin Yan Boko Haram a Borno, Sun Sheƙe Wasu da Yawa

Bala yace: "Yan bindiga sun kai hari ofishin mu dake Izombe, amma jami'an yan sanda dake bakin aiki sun maida martani, sun sami nasarar korar su."

"Huɗu daga cikin waɗanda suka kai harin sun rasa rayukansu a yayin fafatawa da jami'ai, yayin da sauran suka tsere da harbin bindiga a jikin su."

Bala ya ƙara da cewa jami'an yan sanda sun bi bayansu da nufin damƙo ragowar da suka tsere.

A wani labarin kuma Jami'an Tsaro Sun Hallaka Yan Bindiga 4, Sun Cafke Wasu 6 a Rivers

Jami'an tsaro a jihar Rivers sun samu nasarar hallaka yan bindiga biyar tare da damƙe wasu shida daga cikinsu.

Wata majiya daga yankin da abun ya faru tace har yanzun mutanen wajen basu saki jikin su ba saboda harbe-harben da suka ji tsawon dare ɗaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel