Da Ɗumi-Ɗumi: Jami'an Tsaro Sun Hallaka Yan Bindiga 4, Sun Cafke Wasu 6 a Rivers
- Jami'an tsaro a jihar Rivers sun samu nasarar hallaka yan bindiga biyar tare da damƙe wasu shida daga cikinsu
- Wata majiya daga yankin da abun ya faru tace har yanzun mutanen wajen basu saki jikin su ba saboda harbe-harben da suka ji tsawon dare ɗaya
- Kakakin rundunar yan sanda na jihar Rivers, Nnamdi Omoni, ya bayyana cewa har yanzun bashi da rahoto kan lamarin
Akalla yan bindiga biyar ne jami'an tsaro suka miƙa su lahira yayin da suke shirin kai hari Caji ofis ɗin yan sanda dake Ƙaramar hukumar Eleme, jihar Rivers.
KARANTA ANAN: Gwamna Wike Ya Bayyana Matsayarsa Kan Tsayawa Takarar Shugaban Ƙasa a 2023
The nation ta ruwaito cewa jami'an sun kuma samu nasarar damƙe wasu guda shida bayan musayar wuta da ta ɗauki tsawon lokaci.
Rahoton ya bayyana cewa yan bindigan sun yi sansani ne a dajin dake tsakanin Oyigbo da Eleme, inda suke kitsa mummunan shirin su na kai hari ga jami'an yan sanda.
Wata majiya mai ƙarfi, ta bayyana cewa jami'an tsaro na isowa wurin sai yan bindigan suka buɗe musu wuta, inda suma suka maida martani akai artabun da ya shafe lokaci mai tsawo.
Wannan bata kashi ne yayi sanadiyyar mutuwar yan bindiga biyar, sannan aka cafke wasu shida daga cikinsu, kamar yadda vanguard ta ruwaito.
KARANTA ANAN: El-Rufa'I Yayi Magana Kan Sabon Shugaban Sojin Ƙasa Janar Yahaya Faruk, Yace Mutum Ne Mai Juriya
Majiyar tace: "Da yawan yan bindigan waɗanda suka fito daga yankin Oyigbo zuwa Eleme sune aka kashe, an kuma kama sama da mutum shida."
"A yanzu haka da nake magana daku, mazauna yankin na cikin ɗari-ɗari sabida ƙarar harbe-harben da Sukaji tun daren jiya zuwa safiyar yau."
Kakakin hukumar yan sanda na jihar Rivers, Nnamdi Omoni, yace har yanzun bashi da rahoton abinda ya faru.
A wani labarin kuma Rundunar Yan Sanda Ta Fatattaki Yan Bindiga Daga Kai Hari, Ta Sheƙe 4 a Jihar Katsina
Rundunar yan sanda ta bayyana cewa ta samu nasarar hana wasu yan bindiga kai hari Ƙauyen Dangeza jihar Katsina.
Kakakin rundunar na jihar Katsina, SP Gambo Isa, shine ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar.
Asali: Legit.ng