Da Ɗumi-Ɗumi: Sojoji Sun Fatattaki Harin Yan Boko Haram a Borno, Sun Sheƙe Wasu da Yawa

Da Ɗumi-Ɗumi: Sojoji Sun Fatattaki Harin Yan Boko Haram a Borno, Sun Sheƙe Wasu da Yawa

- Awanni kaɗan da kama aikin sabon shugaban rundunar sojin ƙasa, Janar Yahaya Faruk, yan Boko Haram suka yi ƙoƙarin kai hari Borno

- Jami'an sojin Operation haɗin kai sun samu nasarar daƙile harin tare da hallaka yan ta'adda da dama

- Wannan na ƙunshe ne a wani jawabi da kakakin rundunar sojin ƙasa, Muhammed Yerima, ya fitar

Jami'an sojin Operation haɗin kai sun samu nasarar fatattakar mayaƙan Boko Haram tare da sheƙe wasu da dama yayin da suka yi ƙoƙarin kai hari jihar Borno, kamar yadda the nation ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Shugaba Buhari Ya Lashe Kyautar 'Trophée Babacar Ndiaye' Ta Nahiyar Africa 2021

Mayaƙan sun yi ƙoƙarin kai hari garin Rann, hedƙwatar ƙaramar hukumar Kala Balge amma basu samu nasara ba, kamar yadda the cable ta ruwaito.

A jawabin da kakakin rundunar soji ta ƙasa, Muhammed Yerima, ya fitar, yace jami'an sojin sun daƙile harin yan ta'addan yayin da suka yi ƙoƙarin shiga cikin garin.

Da Ɗumi-Ɗumi: Sojoji Sun Fatattaki Harin Yan Boko Haram a Borno, Sun Sheƙe Wasu da Yawa
Da Ɗumi-Ɗumi: Sojoji Sun Fatattaki Harin Yan Boko Haram a Borno, Sun Sheƙe Wasu da Yawa Hoto: @TheNationNews
Asali: Facebook

Wani ɓangaren jawabin yace:

"Awanni kaɗan da shiga ofis ɗin sabon hafsan sojin ƙasa, Mejo Janar Yahaya Faruk, Mayaƙan Boko Haram sun yi ƙoƙarin kai hari kan jami'an sojin Operation haɗin kai a garin Rann, hedkwatar Kala Balge."

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Jami'an Tsaro Sun Hallaka Yan Bindiga 4, Sun Cafke Wasu 6 a Rivers

"Yan ta'addan sun zo da ɗumbin yawa a cikin manyan motocin yaƙi suka yi ƙoƙarin shiga garin, amma jami'an sojin dake cikin shiri suka maida martani, suka fatattake su tare da yi musu mummunar ɓarna."

"Jami'an sun samu nasarar lalata ɗaya daga cikin motocin yaƙin, sannan suka ƙwato makamai da dama, da suka haɗa da, bindigar harbo jirgi, AK-47 guda takwas tare da hallaka aƙalla yan ta'adda takwas."

Jami'an sojin sun bi sawun yan ta'addan domin tabbatar basu sake dawowa kai hari ga jama'ar garin ba.

A wani labarin kuma Gwamna Wike Ya Bayyana Matsayarsa Kan Tsayawa Takarar Shugaban Ƙasa a 2023

Gwamnan Rivers, Nyesom Wike , ya bayyana matsayarsa kan tsayawa takarar shugabancin ƙasar nan a zaɓen 2023 dake tafe.

Wike yace idan yana da muradin tsayawa takara a jam'iyyarsa ta PDP, babu wanda ya isa ya dakatar dashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel