Shugaba Buhari Ya Lashe Kyautar 'Trophée Babacar Ndiaye' Ta Nahiyar Africa 2021

Shugaba Buhari Ya Lashe Kyautar 'Trophée Babacar Ndiaye' Ta Nahiyar Africa 2021

- Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya lashe kyautar gwarzon gina hanyoyi na shekarar 2021

- Shugaban zai amshi kyautar ne daga hannun takwaransa na ƙasar Egypt, Abdul-Fattah Al-Sisi wanda ya lashe shekarar data gabata

- Za'a miƙa kyautar ga wanda ya samu nasara a taron shekara-shekara na bankin AfDB ranar 24 ga watan Yuni

An bayyan shugaba Buhari a matsayin wanda ya lashe lambar yabon "Gwarzon mai gina hanyoyi 2021' wacce akewa laƙabi da Trophée Babacar Ndiaye, kamar yadda the nation ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Jami'an Tsaro Sun Hallaka Yan Bindiga 4, Sun Cafke Wasu 6 a Rivers

Shugaban ƙasar Najeriya ya ƙwace kyautar ne daga hannun shugaban ƙasar Egypt, Abdul Fatta Al-sisi wanda ya lashe kyautar a shekarar 2020.

A jawabin da bankin Africa AfDB ya fitar jiya, yace an bayyana sunan Buhari a matsayin wanda ya lashe kyautar a wajen buɗe taron masu gina hanyoyi ranar 31 ga watan Maris a Cairo, Egypt.

Shugaba Buhari Ya Lashe Kyautar 'Trophée Babacar Ndiaye' Ta Nahiyar Africa 2021
Shugaba Buhari Ya Lashe Kyautar 'Trophée Babacar Ndiaye' Ta Nahiyar Africa 2021 Hoto: @BashirAhmad
Asali: Twitter

Hakanan kuma za'a bada kyautar ne ga wanda ya samu nasara a babban taron shekara-shekara na bankin AfDB da zai gudana ranar 24 ga watan Yuni.

Al-sisi ya lashe kyautar ne saboda "Kyakkyawn shugabancinsa da ƙoƙarin gwmanatinsa wajen kiyaye hanyoyi da kare lafiyar al'umma yayin tafiye-tafiye."

Kwamitin zaɓe, sun zaɓo Najeriya ne saboda ƙara inganta hanyoyinta ga matafiya na ƙasa da kuma na sama.

KARANTA ANAN: Gwamna Wike Ya Bayyana Matsayarsa Kan Tsayawa Takarar Shugaban Ƙasa a 2023

Kwamitin ya kuma yaba da ƙoƙarin Najeriya dangane da samar da rigakafin COVID19 da kuma faɗaɗa ayyukan hanyoyinta musamman a ɓangaren hanyoyin jirgin ƙasa.

Kwamitin masu zaɓen ya haɗa da wakilan kafofin yaɗa labarai daga yankuna biyar na nahiyoyin duniya, waɗanda suka ƙware da masana ingancin hanyoyi da tafiye-tafiye.

An ƙirƙiri wannan kyautar ne domin nuna girmmawa ga shugaban AfDB, Babacar Ndiaye, daga 1985 zuwa 1995.

A wani labarin kuma El-Rufa'I Yayi Magana Kan Sabon Shugaban Sojin Ƙasa Janar Yahaya Faruk, Yace Mutum Ne Mai Juriya

Gwamnan Kaduna , Malam Nasiru El-Rufa'i, ya nuna matuƙar farin cikinsa da naɗin Mejo Janar Yahaya Faruk a matsayin sabon COAS, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Gwamnan ya bayyana shi da mutum mai juriya da hangen nesa wajen nemo hanyoyin magance ƙalubalen tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel