El-Rufa'I Yayi Magana Kan Sabon Shugaban Sojin Ƙasa Janar Yahaya Faruk, Yace Mutum Ne Mai Juriya

El-Rufa'I Yayi Magana Kan Sabon Shugaban Sojin Ƙasa Janar Yahaya Faruk, Yace Mutum Ne Mai Juriya

- Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i, ya nuna matuƙar farin cikinsa da naɗin Mejo Janar Yahaya Faruk a matsayin sabon COAS

- Gwamnan ya bayyana shi da mutum mai juriya da hangen nesa wajen nemo hanyoyin magance ƙalubalen tsaro

- Gwamnan, amadadin al'unnar jiharsa sun miƙa saƙon taya murna ga sabon COAS Yahaya Faruk

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i, ya taya sabon shugaban dakarun sojin ƙasa Mejo Janar Yahaya Faruk, yace mutum ne mai jure wa wahala da hangen nesa wajen sarrafa ƙalubalen tsaron ƙasa.

KARANTA ANAN: Matsalar Tsaro: Mun Cafke Masu Aikata Manyan Laifuka Sama da 1,000 Cikin Wata Ɗaya Kacal, IGP

Kwamishinan tsaro na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, shine ya bayyana haka a wani jawabin murna da ya fitar Ranar Alhamis, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Gwamnan yace yana taya sabon hafsan sojin ƙasa murna bisa wannan matsayi da ya taka kuma yana mishi fatan nasara wajen kawo cigaba ga rundunar soji, da kuma ɗorawa daga inda marigayi Ibrahim Attahiru ya tsaya.

El-Rufa'I Yayi Magana Kan Sabon Shugaban Sojin Ƙasa Janar Yahaya Faruk, Yace Mutum Ne Mai Juriya
El-Rufa'I Yayi Magana Kan Sabon Shugaban Sojin Ƙasa Janar Yahaya Faruk, Yace Mutum Ne Mai Juriya Hoto: @Govkaduna
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Minista Tayi Magana Kan Shirin N-Power, Tace an Biya Dukkan Ma’aikata Haƙkinsu

Jawabin yace: "Gwamnan Kaduna yayi farin ciki da naɗin Mejo Janar Faruk, sabida yayi aiki dashi lokacin da yake kwamanda janar na runduna ta 1, wanda ta haɗa jihohin Kaduna, Jigawa, Neja, da Kano."

"Sabon hafsan sojin yana da juriya da hangen nesa wajen taimakawa a fuskanci ƙalubalen tsaro a jihar Kaduna lokacin da yake GOC."

"Gwamna El-Rufa'i, amadadin al'ummar jihar Kaduna suna miƙa saƙon taya murna ga sabon hafsan sojin ƙasa kuma suna mai fatan nasara da tsarin Allah a aikinshi."

"Gwamnatin jihar Kaduna a shirye take wajen aiki da sabon COAS domin kawo zaman lafiya da tsaro a jihar Kaduna."

A wani labarain kuma Rundunar Yan Sanda Ta Fatattaki Yan Bindiga Daga Kai Hari, Ta Sheƙe 4 a Jihar Katsina

Rundunar yan sanda ta bayyana cewa ta samu nasarar hana wasu yan bindiga kai hari Ƙauyen Dangeza jihar Katsina.

Kakakin rundunar na jihar Katsina, SP Gambo Isa, shine ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel