FG ta bayyana dalilin da yasa Buhari ya nada Yahaya a matsayin shugaban hafsan soji

FG ta bayyana dalilin da yasa Buhari ya nada Yahaya a matsayin shugaban hafsan soji

- Akwai karin bayanai game da dalilin da yasa aka nada Manjo-Janar Farouk Yahaya a matsayin sabon shugaban hafsan soji

- Ministan tsaro, Manjo-Janar Bashir Salihi-Magashi (mai ritaya) ya ba da karin haske game da abin da ya sa Shugaban kasar ya yanke shawarar hakan

- Salihi-Magashi ya bayyana cewa iya aiki da kwazon isar da shi shine babban abunda ke zuciyar shugaban kasar yayin zabar sabon shugaban sojoji

Gwamnatin tarayya ta bayyana dalilin da ya sa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Manjo Janar Faruk Yahaya a matsayin sabon shugaban hafsan soji.

Gwamnatin ta yi wannan bayanin ne ta bakin Ministan Tsaro, Manjo-Janar Bashir Salihi-Magashi (mai ritaya) a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, 28 ga watan Mayu.

KU KARANTA KUMA: Tubabbun yan bindiga sun ajiye makamai sama da 1000, gwamnatin jihar Zamfara

FG ta bayyana dalilin da yasa Buhari ya nada Yahaya a matsayin shugaban hafsan soji
FG ta bayyana dalilin da yasa Buhari ya nada Yahaya a matsayin shugaban hafsan soji Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Sanarwar da mai magana da yawun ministan, Mohammad Abdulkadri ya fitar, kuma Legit.ng ta gani, ta ce Shugaba Buhari ya yi zabin ne saboda kishin kasa da kuma bukatar hadin kan kasa.

Ministan ya ce:

Shugaba Buhari ya fifita bukatun kasa fiye da kabilanci da addini ta hanyar cika dukkan abubuwan da ake bukata.

Ministan tsaron ya kuma nuna kwarin gwiwa a bangaren kwarewar COAS din wajen ci gaba da daukar matakan kai hare-hare da zagon kasa ga sansanoni, farfajiyoyi, da kuma sel din abokan adawar Najeriya da nufin kawar da su.

KU KARANTA KUMA: Tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kai wa Buhari ziyara a Abuja

A gefe guda, Legit.ng ta kawo cewa Manjo Janar Farouq Yahaya a ranar Juma’a 28 ga Mayu, ya fara aiki a matsayin Shugaban Sojojin Najeriya na 22 a Hedikwatar Soji da ke Abuja.

Ya fara aikinsa ne ta hanyar duba masu tsaron Kwatas din Channels TV ta ruwaito.

A ranar Alhamis 27 ga watan Mayu ne hedikwatar tsaron ta sanar da nadin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa Yahaya a matsayin sabon COAS.

A wani labarin kuma, mun ji cewa lokacin da aka dauke Farouk Yahaya daga runduna ta 1 ta sojojin Najeriya a jihar Kaduna don lura da yake-yake da ake yi da Boko Haram a arewa maso gabas, ya yi alkawarin tabbatar da “cikakken zaman lafiya da nutsuwa” a yankin da ke fama da rikici.

Zai yiwu bai sami nasarar hakan kwata-kwata ba, amma abubuwa sun inganta a karkashin kulawarsa duba ga rubutattun bayanai, in ji The Cable.

Bayanai sun nuna cewa daga ranar da ya fara jagorantar yaki da Boko Haram, har zuwa ranar da aka nada shi COAS yawan fararen hular da maharan suka kashe ya ragu da 17% cikin 100%, in ji Majalisa kan Harkokin Kasashen Waje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel