Yanzu Yanzu: Manjo Janar Farouq Yahaya ya kama aiki a matsayin Shugaban hafsan soji na 22

Yanzu Yanzu: Manjo Janar Farouq Yahaya ya kama aiki a matsayin Shugaban hafsan soji na 22

- Bayan murnar nadin nasa, Manjo Janar Yahaya a yanzu ya fara aikinsa na tsare Najeriya a hukumance

- Shugaban hafsan soji na 22 ya fara aiki ne a hedikwatar rundunar dake Abuja a ranar Juma’a, 28 ga Mayu

- Da farko, Yahaya ya karrama magabacinsa, Ibrahim Attahiru, wanda kwanan nan ya mutu a wani hatsarin jirgin sama

Manjo Janar Farouq Yahaya a ranar Juma’a 28 ga Mayu, ya fara aiki a matsayin Shugaban Sojojin Najeriya na 22 a Hedikwatar Soji da ke Abuja.

Ya fara aikinsa ne ta hanyar duba masu tsaron Kwatas din Channels TV ta ruwaito.

A ranar Alhamis 27 ga watan Mayu ne hedikwatar tsaron ta sanar da nadin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa Yahaya a matsayin sabon COAS.

KU KARANTA KUMA: Labarin ma'aikacin otel da ya tsinci damin daloli a dakin baƙi kuma ya mayar ya jawo cece kuce

Yanzu Yanzu: Manjo Janar Farouq Yahaya ya kama aiki a matsayin Shugaban hafsan soji na 22
Yanzu Yanzu: Manjo Janar Farouq Yahaya ya kama aiki a matsayin Shugaban hafsan soji na 22 Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Sabon COAS da aka nada a baya ya kai ziyarar karramawar karshe ga tsohon shugabansa kuma wanda ya gada, Lt-Gen Ibrahim Attahiru.

Manjo-Janar Yahaya ya yi mubaya'a ga marigayi Attahiru ne bayan sanya hannu a rajistar ta'aziyar a hedkwatar rundunar Operation Hadin Kai da ke yankin Maimalari, Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Attahiru da wasu hafsoshin soja 10 sun mutu a wani hatsarin jirgin sama a Kaduna a ranar Juma'a, 21 ga Mayu.

KU KARANTA KUMA: Daga Abdulsalami zuwa Buhari: Jaddawalin kuɗaɗen da aka ƙwato waɗanda Abacha ya sace daga 1998

'Yan Najeriya sun taya Yahaya murna

Ray Momoh ya ce:

"Ina taya ka murna. Ka tuna soja ya tafi, Soja ya zo. Bariki na nan ci gaba da iyakar kokarin ka ta hanyar mutunta 'yancin yan Najeriya"

Godfrey Gantip ya ce:

"Ina taya ka murna, Tarin Alheri da Hikimar Allah a gare ka kuma ina rokon Allah ya kare dukkan Sojojin Najeriya"

Fakolade Oluwafemi Temitope ya ce:

"Ina taya ka murna yallabai. Da fatan kariyar Allah madaukakin sarki ta kasance a kanka da kuma dukkanin tawagarka"

A gefe guda, Kungiyar nan ta Human Rights Writers Association of Nigeria wanda aka fi sani da HURIWA, ta yi magana a game da nadin sabon hafsun sojan kasa.

A ranar Alhamis, 27 ga watan Mayu, 2021, jaridar Punch ta rahoto kungiyar masu kare hakkin Bil Adama ta kasar tana sukar shugaba Muhammadu Buhari.

HURIWA ba ta ji dadin yadda shugaban kasa ya sake nada sojan Arewa a matsayin sabon hafsun sojan kasa ba, ta so ace an zakulo hafsun daga yankin Ibo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel