Sabon Hafsan Sojoji Yahaya Ya Kashe Sama Da ’Yan Boko Haram 2,000 a Fagen Yaki

Sabon Hafsan Sojoji Yahaya Ya Kashe Sama Da ’Yan Boko Haram 2,000 a Fagen Yaki

- Rundunar sojin Najeriya a yau, Alhamis 27 ga watan Mayu ta yi sabon shugaban hafso da zai jagorance ta

- Rahotanni sun bayyana cewa, Manjo-Janar Farouk Yahaya jami'i ne mai jajircewar gaske, tare da gwazo

- Rahoto ya bayyana cewa, akalla 'yan Boko Haram 2000 aka hallaka a karkashin jagorancinsa

Lokacin da aka dauke Farouk Yahaya daga runduna ta 1 ta sojojin Najeriya a jihar Kaduna don lura da yake-yake da ake yi da Boko Haram a arewa maso gabas, ya yi alkawarin tabbatar da “cikakken zaman lafiya da nutsuwa” a yankin da ke fama da rikici.

Zai yiwu bai sami nasarar hakan kwata-kwata ba, amma abubuwa sun inganta a karkashin kulawarsa duba ga rubutattun bayanai, in ji The Cable.

Bayanai sun nuna cewa daga ranar da ya fara jagorantar yaki da Boko Haram, har zuwa ranar da aka nada shi COAS yawan fararen hular da maharan suka kashe ya ragu da 17% cikin 100%, in ji Majalisa kan Harkokin Kasashen Waje.

KU KARANTA: Sabon Nadi: Sharhin 'Yan Najeriya Game da Nada Manjo-Janar Farouk Yahaya

Yahaya, Sabon Hafsan Sojoji Ya Kashe Sama Da ’Yan Boko Haram 2,000 a Fagen Yaki
Yahaya, Sabon Hafsan Sojoji Ya Kashe Sama Da ’Yan Boko Haram 2,000 a Fagen Yaki Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Hakazalika, adadin 'yan Boko Haram din da aka kashe ya tashi da 46% cikin 100%.

Bayanan, wadanda aka tattara daga rahotannin kafofin watsa labarai, ya nuna cewa maharan sun kashe mutane 946 daga lokacin da aka nada shi kwamanda na sabon aikin da aka sauya wa suna zuwa Operation Hadin Kai idan aka kwatanta da 1,137 da suka mutu a cikin watanni 14 da suka gabata.

A gefen kungiyar 'yan ta'adda, an bayar da rahoton cewa an kashe mambobi 2,122 a lokacin jagorancin Yahaya, idan aka kwatanta da 1,449 da aka kashe a cikin lokacin da ya gabata.

Duk da cewa, maharan sun kaddamar da hare-hare da dama yayin da Yahaya ke jagoranci, kamar a karshen watan Afrilu lokacin da suka tilasta dubban mazauna Geidam ta jihar Yobe tserewa zuwa Jamhuriyar Nijar yayin wani harin da ya dauki kwanaki.

A rawar da yake takawa a rundunar sojojin Najeriya, Yahaya ya kan nemi kari daga ma’aikatan da ke karkashin sa.

Lokacin da ya karbi aiki daga Mohammed Mohammed a matsayin babban kwamandan GOC na 1 a Kaduna, ya gaya wa sojoji da jami'ai a bangarensa cewa dole ne su bi ka'idojin aiki.

Ya taba cewa:

"Ba na tsammanin komai sai dai kari,"
“Ina yi muku wasiyya da cewa dukkanku ku dage. Yakamata mu kasance masu gudun siyasa kuma mu jajirce kan yankunan da suke karkashin kulawarmu. Wajibi ne ku gudanar da ayyukanku yadda ya kamata kuma ku kasance kwararru a yayin gudanar da ayyukanku.”

A ranar 5 ga Fabrairun, lokacin da aka bayar da rahoton kashe maharan Boko Haram sama da 50, Yahaya ya ce wa sojoji kada su ja da baya saboda yanzu aka fara..

“Kada ku zama masu lalaci da mutuwar jiki. Lokacin da kuka ga 'yan ta'adda, to ku tunkare su ku yi maganinsu. Ku bi su, kada ku tausaya rayukansu,"

KU KARANTA: Lai Mohammed Ga ’Yan Najeriya: Ku Kwantar da Hankali, Najeriya Na Cikin Aminci

A wani labarin, Kimanin Manjo-Janar 10 na Sojojin Najeriya ake sa ran za su yi ritaya daga aiki biyo bayan nada Manjo-Janar Farouk Yahaya a matsayin Babban Hafsan Sojoji na 22.

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Yahaya a ranar Alhamis don maye gurbin marigayi Laftanar Janar Ibrahim Attahiru, wanda ya mutu tare da wasu hafsoshin soja 10 a wani hadarin jirgin saman soja a Kaduna a ranar Juma’ar da ta gabata, in ji hedkwatar soji.

Akwai akalla Manjo-Janar 10 daga kwasa-kwasan 35 da 36 har yanzu a cikin Sojojin Najeriya bisa ga bayanai da aka samu, Sahara Reporters ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel