Tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kai wa Buhari ziyara a Abuja

Tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kai wa Buhari ziyara a Abuja

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin tsohon Shugaban kasar, Goodluck Ebele Jonathan a fadar Villa

- Jonathan ya je fadar shugaban kasar ne bayar da jawabi a kan rikicin shugabancin da ke faruwa a kasar Mali

- Idan za ku tuna, tawagar ECOWAS da Jonathan ya jagoranta sun sauka Bamako babban birnin Mali a ranar Talata domin shiga tsakani

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin tsohon Shugaban kasar, Goodluck Ebele Jonathan a yau Juma’a, 28 ga watan Mayu, a fadar shugaban kasa da ke babbar birnin tarayya, Abuja.

Tsohon shugaban ya ziyarci Shugaban kasar ne domin ba shi bahasi a kan rikicin shugabancin da ke faruwa a kasar Mali kamar yadda hadimin Shugaban kasa a shafukan zumunta na zamani, Bashir Ahmed ya wallafa a shafinsa na Twitter.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Manjo Janar Farouq Yahaya ya kama aiki a matsayin Shugaban hafsan soji na 22

Tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kai wa Buhari ziyara a Abuja
Tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kai wa Buhari ziyara a Abuja Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Ya kuma bayyana cewa wata tawagar ECOWAS da Jonathan ya jagoranta sun sauka Bamako babban birnin Mali a ranar Talata domin shiga tsakani.

Ya wallafa a shafinsa:

“Shugaban kasa @Mbuhari ya tarbi tsohon Shugaban kasa @GEJonathan yau. Tsohon shugaban kasar ya kasance a Fadar Shugaban Kasa, Abuja don yi wa Shugaban kasar bayani game da sabon rikicin siyasar kasar ta Mali.
“Wata tawagar ECOWAS karkashin jagorancin GEJ ta kasance a Bamako, babban birnin Mali ranar Talata, don sasantawa.”

Da yake tabbatar da ganawar tasu, Shugaba Buhari ya ce:

Na hadu da tsohon Shugaba Jonathan a safiyar yau, game da halin da ake ciki a Mali, inda shi ne wakili na musamman kuma Mai shiga tsakani na ECOWAS.
Ina kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su hallara domin tabbatar da zaman lafiya, hadin kai da tsaro a kasar ta Mali. Ba za mu iya ɗaukar ci gaban wannan rikici ba.

Legit.ng ta tattaro wasu martanin da jama'a suka yi kan ziyarar:

@AustineJohnsonA ya yi martani:

Tawali'u da ke cikin shugaba Good luck Jonathan ba shi da na biyu, mutumin ya ci gaba da yi wa Najeriya bauta da aiki har ma bayan cin mutunci da cin amanarsa da yawancin ofisoshinsa da membobin jam'iyyar suka yi. Ina jinjina maka Gej!

@godsonOVD ya ce:

Buhari ba zai yi irin wannan ba idan akasin haka ne .... amma a maimakon haka sai ya kara dagula lamirinsa.

@jahbless1986 ya ce:

Menene manufar GEJ a Mali. Mali Mali kowane lokaci kamar ƙasarsa ba ta samun rikici.

Jonathan ya shiga-ya fita har sai da Sojojin tawaye suka fito da Shugabannin Mali da suka tsare

Legit.ng ta kawo cewa yunkurin sasancin da tsohon shugaban Najeriya, Dr. Goodluck Jonathan yake yi wajen kawo karshen rikicin kasar Mali, ya na haifar da ‘da mai ido.

KU KARANTA KUMA: Daga Abdulsalami zuwa Buhari: Jaddawalin kuɗaɗen da aka ƙwato waɗanda Abacha ya sace daga 1998

Jaridar Punch ta ce wannan kokari na Goodluck Jonathan ya yi nasarar fito da shugaban rikon kwarya da Firayim Ministan Mali da sojoji suka tsare.

A wani jawabi da ya fito daga ofishin yada labarai na Goodluck Jonathan a ranar Alhamis, 27 ga watan Mayu, 2021, an yi bayanin rawar ganin da ya taka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng