Tubabbun yan bindiga sun ajiye makamai sama da 1000, gwamnatin jihar Zamfara

Tubabbun yan bindiga sun ajiye makamai sama da 1000, gwamnatin jihar Zamfara

- Gwamnatin Zamfara ta lissafa jeringiyar nasarorin da ta samu sakamakon sulhu da yan bindiga

- A cikin makon nan, jihar ta samu ceto mutum 76 ba tare da biyan kudin fansa ba

- Jihar Zamfara na cikin jihohin dake fama da matsalar tsaro a Arewacin Najeriya

Gwamnatin jihar Zamfara ta ce tubabbun yan bindigan da suka addabi jihar a baya kawo yanzu sun ajiye makamai sama da dubu guda karkashin shirin sulhun da gwamnatin ta yi.

Kwamishanan tsaro da harkokin cikin gidan jihar, Garba Dauran, ya bayyana hakan ga manema labarai a Gusau, birnin jihar.

Dauran ya ce an lissafa jerin kananan da manyan makamai da albursai da yan bindigan suka ajiye.

A cewarsa, wadannan makamai sun hada da:

1. Bindigogin gargajiya 887

2. Manyan makami 203

3. Albursai 2,566

4. Akwatin lodin albursai na AK-47 guda 64

5. Ankwa 2

KU KARANTA: Nan da watan Yuli zamu fara ginin layin dogon Kaduna zuwa Kano, Minista Amaechi

Tubabbun yan bindiga sun ajiye makamai sama da 1000, gwamnatin jihar Zamfara
Tubabbun yan bindiga sun ajiye makamai sama da 1000, gwamnatin jihar Zamfara Hoto: @tvcnewsng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Mun Cafke Duk Wani Mai Hannu a Harin da Aka Kaiwa Gwamnan Benuwai, IGP

A riwayar Daily Nigerian, kwamishanan ya yi kira da shugabannin gargajiya su taimaka wajen lura da yankunansu don gano yan bindiga.

A ranar 7 ga Febrairu, gwamnatin jihar Zamfara ta shiga sulhu da yan bindigan da suka addabi jihar domin neman saukin hare-hare.

DUBA NAN: Gwanda mu daina yaudarar kanmu, abubuwa sun tabarbare a kasar nan: Sarkin Musulmi

A bangare guda, mutum saba'in da shida da aka yi garkuwa da su a garin Yarkatsina a karamar hukumar Bungudu na jihar Zamfara sun samu yanci, gwamnatin jihar ta tabbatar.

Gwamnatin jihar ta ce yan bindigan sun saki wadanda suka sace ne ba tare da biyan kudin fansa ba bayan sulhu da ita.

Mutanen da aka sace yawancinsu mata da yara ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel