Daga Abdulsalami zuwa Buhari: Jaddawalin kuɗaɗen da aka ƙwato waɗanda Abacha ya sace daga 1998

Daga Abdulsalami zuwa Buhari: Jaddawalin kuɗaɗen da aka ƙwato waɗanda Abacha ya sace daga 1998

- Marigayi Janar Sani Abaja ya shugabanci Najeriya a mulkin soja tsakanin 1993 da 1998

- Bayan rasuwarsa an ta gano kudaden da ya boye a kasashe daban-daban

- Legit.ng ta lissafo jaddawalin kuɗaɗen da aka ƙwato waɗanda tsaohon shugaban kasar ya sace a wannan zauren

"Idan ba mu kashe rashawa ba, rashawa za ta kashe Najeriya," Shugaba Muhammadu Buhari ya fada akai-akai.

Sani Abacha ya yi aiki a matsayin shugaban kasa a mulkin sojan Najeriya daga 1993 zuwa rasuwarsa a 1998. Sai dai, tun bayan rasuwarsa, Najeriya na ci gaba da dawo da biliyoyin nairorin da ya sata a kasashe daban-daban wadanda a yanzu ake wa lakabi da 'Abacha loots'.

KU KARANTA KUMA: Manjo-Janar Yayaha: Jerin Manyan Hafsoshin Sojojin Kasar Tun Daga Shekarar 1999

Daga Abdulsalami zuwa Buhari: Jaddawalin kuɗaɗen da aka ƙwato waɗanda Abacha ya sace daga 1998
Daga Abdulsalami zuwa Buhari: Jaddawalin kuɗaɗen da aka ƙwato waɗanda Abacha ya sace daga 1998 Hoto: ISSOUF SANOGO/AFP
Asali: Getty Images

Wannan zauren ya lissafa "ganimar Abacha" da aka kwato a karkashin gwamnatocin da suka gabata daga 1998 zuwa 2020, inda aka ambaci wani rahoto na The Cable.

1. Abdulsalami Abubakar (Dala miliyan 750)

Abdulsalami Abubakar ya gaji Abacha a 1988 kuma ya jagoranci mika mulki zuwa dimokuradiyya a 1999. A cikin 1988, ya kwato dala miliyan 750 daga dangin Abacha.

2. Olusegun Obasanjo

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya mulki Najeriya daga 1999 zuwa 2007. A 2000, ya kwato dala miliyan 64 na kudin satan daga Switzerland.

A 2002, Obasanjo ya dawo da dala biliyan 1.2 ta hanyar yarjejeniyar dangin Abacha.

A shekarar 2003, tsohon shugaban kasar ya kuma gano dala miliyan 160 daga Jersey, British Island da dala miliyan 88 daga Switzerland.

Obasanjo ya kuma kwato dala miliyan 461 daga Switzerland a 2005 da dala miliyan 44 daga kasar a 2006.

KU KARANTA KUMA: Bidiyon sojoji sun kacame da murna bayan an sanar da Farouk Yahaya matsayin COAS

3. Goodluck Jonathan

A shekarar 2014, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kwato dala miliyan 227 daga Liechtenstein.

4. Muhammadu Buhari

A shekarar 2018, Shugaba Muhammadu Buhari ya kwato dala miliyan 322 daga Switzerland yayin da a shekarar 2020, ya gano dala miliyan 308 daga Jersey/Amurka.

Adadin kudin da aka kwato ya zuwa yanzu ya kusan dala biliyan 3.624.

A wani labarin, mun ji cewa daga watan Yulin 2015 zuwa karshen shekarar Disamban 2020, adadin bashin da ke kan wuyan gwamnatin Najeriya ya tashi da Naira tiriliyan 20.8.

Jaridar Punch ta ce alkaluman da ta samu daga ofishin tattara bashi na kasa, DMO, ya nuna haka. Gwamnatin tarayya ce ta ci duk mafi yawan bashin nan da ake magana.

Sama da 80% na bashin da ake bin kasar ya na kan wuyan gwamnatin tarayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel