Kungiya ta yi kaca-kaca da Shugaba Buhari a kan nadin sabon shugaban Sojojin kasa

Kungiya ta yi kaca-kaca da Shugaba Buhari a kan nadin sabon shugaban Sojojin kasa

- HURIWA da Ohanaeze Ndigbo Worldwide sun yi tir da nadin sabon COAS

- Zaben Janar Farouk Yahaya ya jawo ana kukan an yi watsi da Ibo

- Kungiyoyin sun ce gwamnatin Buhari ta na fifita kabilar Hausa da Fulani

Kungiyar nan ta Human Rights Writers Association of Nigeria wanda aka fi sani da HURIWA, ta yi magana a game da nadin sabon hafsun sojan kasa.

A ranar Alhamis, 27 ga watan Mayu, 2021, jaridar Punch ta rahoto kungiyar masu kare hakkin Bil Adama ta kasar tana sukar shugaba Muhammadu Buhari.

HURIWA ba ta ji dadin yadda shugaban kasa ya sake nada sojan Arewa a matsayin sabon hafsun sojan kasa ba, ta so ace an zakulo hafsun daga yankin Ibo.

KU KARANTA: Jami’an Arewa 20 da su ka rike mukamin Hafsoshin sojin kasa a tarihi

Kungiyar a jawabin da ta fitar, ta ce: “Mun daina mamakin tsantsagwaron son kan da shugaban kasa Buhari yake nuna wa.”, ta ce nadin da aka yi ya saba doka.

Shugaban kungiyar HURIWA na kasa, Emmanuel Onwubiko, ya fitar da jawabi inda ya yi Allah-wadai da rashin dauko wani jami’i daga yankin Kudu maso gabas.

Onwubiko yake cewa hakan ya nuna shugaba Muhammadu Buhari bai yarda Najeriya kasa daya ba ce. Jaridar Independent ta dauko wannan rahoto a jiya da yamma.

Har ila yau, kungiyar mutanen kasar Ibo, Ohanaeze Ndigbo Worldwide, ta soki nadin da aka yi, ta ce sam gwamnatin Muhammadu Buhari ba ta kaunar tafiya da Ibo.

KU KARANTA: Sojoji sun yi murnar zaben F. Yahaya a matsayin sabon COAS

Kungiya ta yi kaca-kaca da Shugaba Buhari a kan nadin sabon shugaban Sojojin kasa
Manjo Janar Farouk Yahaya
Asali: Facebook

Daga cikin hafsoshin sojoji hudu da sufetan ‘yan sanda da aka nada a shekarar nan, Ibo guda rak aka samu, wannan ya sa kungiyar Ohanaeze Ndigbo take banbami.

A cewar kungiyar Ohanaeze Ndigbo Worldwide, yadda gwamnatin APC mai-ci ta maida mutanenta saniyar ware ne ya jawo wasu suke cewa a raba Najeriyar.

Manjo Janar Farouk Yahaya da aka nada jiya ya fito ne daga bangaren Arewacin Najeriya kamar sauran hafsoshin da aka yi kafinsa, Ibrahim Attahiru da Tukur Buratai.

A jiya ne ta tabbata cewa shugaba Muhammadu Buhari ya nada Farouk Yahaya a matsayin sabon shugaban hafsan sojin kasa bayan mutuwar Janar Attahiru Ibrahim.

Manjo Janar Farouk Yahaya shi ne shugaban rundunar Operation Hadin Kai dake yaki da 'yan ta'adda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng