Raba Kaduna Gida Biyu: Arewaci da Kudancin Kaduna Sun Amince Su Yi Hannun Riga

Raba Kaduna Gida Biyu: Arewaci da Kudancin Kaduna Sun Amince Su Yi Hannun Riga

- Yankin kudancin kaduna da kuma na arewaci sun amince da rabewa zuwa kafa karin sabbin jihohi biyu

- Shugaban kungiyar Kudancin Kaduna (SOKAPU), Jonathan Asake ne ya bayyana hakan a ranar Laraba

- Dukkanin bangarorin na da ra’ayin cewa kirkirar jihar zai taimaka sosai wajen samar da dawwamammen zaman lafiya a Kaduna

Wani rahoto da jaridar Nigerian Tribune ta fitar ya nuna cewa kungiyar Kudancin Kaduna (SOKAPU) da takwararta ta arewa sun amince da raba Kaduna zuwa sabbin jihohi biyu.

Jonathan Asake, shugaban kungiyar SOKAPU ne ya bayyana hakan yayin gabatarwa da kuma kare bukatunsu a kwamitin wucin gadi na majalisar dattijai da kuma majalisar wakilai ta musamman kan sake duba kundin tsarin mulkin 1999 a bangaren shari'a.

KU KARANTA: Gwamna a Najeriya: Ba Na Karbar Albashi a Matsayi na Gwamna, Aiki Kawai Nake

Raba Kaduna Gida Biyu: Arewaci da Kudancin Kaduna Sun Amince Su Yi Hannun Riga
Raba Kaduna Gida Biyu: Arewaci da Kudancin Kaduna Sun Amince Su Yi Hannun Riga Hoto: thewhistler.ng
Asali: UGC

Da yake magana yayin gabatarwar, a ranar Laraba, 26 ga watan Mayu, shugaban kungiyar ta SOKAPU ya ce burin kudancin Kaduna shi ne a samar da sabon kundin tsarin mulki, ba wai gyara tsoho ba.

A cewarsa, mutanen da suka sha wahalar danniya da tsangwama na tsawon lokaci suna yin abubuwan da suke sanyawa a matsayin mutane yayin da babu wani sabon kundin tsarin mulki, inji rahoton Sun News.

Ya kuma bayyana koken yankin kudancin Kaduna na kasancewa a hade na tsawon lokaci, tare da jaddada bukatarsu da ta jima sama da shekaru 30.

KU KARANTA: Ministan Buhari: Idan Talakawa Suka Nemi Na Tsaya Takarar Shugabanci 2023, Zan Yi

A wani labarin, Fusattatun dalibai a jami’ar jihar Kaduna (KASU) a ranar Laraba sun gudanar da wata zanga-zangar lumana a babban harabar makarantar kan shirin da gwamnati ke yi na kara kudin makaranta daga N35,000 zuwa mafi karancin N150,000.

Daliban sun yi zargin cewa karin wani yunkuri ne na hana su hakkinsu na samun ilimi a matsayinsu na 'yan kasa, The Nation ta ruwaito.

Sun bayyana matakin da gwamna Nasir El-Rufai ya dauka a matsayin ganganci na kokarin sanya ilimi ya gagari 'ya'yan talakawa baya ga tuhumar kara kudin dakunan kwanan dalibai zuwa N80,000 da kuma korar iyayensu da za su ke daukar nauyinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.