Sabon Nadi: Sharhin 'Yan Najeriya Game da Nada Manjo-Janar Farouk Yahaya

Sabon Nadi: Sharhin 'Yan Najeriya Game da Nada Manjo-Janar Farouk Yahaya

- 'Yan Najeriya sun tofa albarkacin bakinsu bayan da shugaba Buhari ya nada sabon shugaban hafsan soji

- Wasu daga ciki na yabo, wasu kuwa kushe sabon nadin suke yi saboda a ganinsu hakan bai yi daidai da bukatarsu ba

- Legit.ng Hausa ta tattaro muku sharhin da 'yan Najeriya suka zuba game da Manjo-Janar Farouk Yahaya

A yau ne rundunar sojin Najeriya ta yi sabon shugaban hafsan soji bayan rasuwar tsohon jami'i Laftanar-Janar Ibrahim Attahiru.

Wata sanarwa da hedkwatar tsaro ta sojin Najeriya ta bayyana cewa, an nada Manjo-Janar Farouk Yahaya a matsayin sabon shugaban hafsan soji.

Shin meye 'yan Najeriya ke cewa game da sabon nadin na shugaban hafsan soji? Legit.ng Hausa ta tattaro sharhin 'yan Najeriya game da sabon nadin.

KU KARANTA: Da duminsa: Shugaba Buhari ya nada sabon shugaban sojin kasa

Sharhin 'Yan Najeriya Game da Nada Manjo-Janar Farouk Yahaya
Sharhin 'Yan Najeriya Game da Nada Manjo-Janar Farouk Yahaya Hoto: blueprint.ng
Asali: UGC

@FS_Yusuf_ yace:

"Yanzu-yanzu: Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Manjo Janar Farouk Yahaya a matsayin sabon shugaban hafsan soji.

"Ni ma ina son Buhari. Ba ya canzawa game da gaskiyar cewa akwai nade-naden da ba zai taba ba wa kirista na kudu ba ko ma Kirista na Arewa."

@bulamabukarti mai sharhi kan lamuran yau da kullum ya rubuta:

"Shugaba Buhari ya nada Manjo Janar Farouk Yahaya, kwamandan rundunar Operation Hadin Kai mai ci, a matsayin shugaban hafsan soji. Operation Hadin Kai itace rundunar da ke yaki da Boko Haram. Wannan wata kila manuniya ce game da fifikon da Buhari ya ba rikicin Boko Haram."

@dawisu, tsohon hadimin gwamna Ganduje shi kuwa cewa ya yi:

"Jinjina ga Manjo Janar Farouk Yahaya, sabon shugaban hafsan sojan da aka nada. Allah Ya yi maka jagora, Ya kiyaye ka. Ina maka fatan isar da babban aikinka na jagorancin sojojin Najeriya. Allah sa albarka amin."

@chosensamto daga yankin kudanci shi kuwa sukar nadin ya yi, ya ce:

"Sabon Babban hafsan sojan kasa shi ne Manjo Janar Farouk Yahaya.

"Da alama babu wani daga Kudu da ya cancanci matsayin COAS a cikin shekaru 6 da suka gabata.

Gobe APC za ta yi kamar ba ta san yadda ta raba Najeriya ta dora mu a kan turbar yaki ba."

@ogundamisi kuwa cewa ya yi:

"Fatan Manjo-Janar Farouk Yahaya da duk jajirtattun Maza da Mata na Sojojin Nijeriya da zai jagoranta, mafi kyau.

"Sojojinmu suna sadaukar da tasu rayuwar, wani lokacin suna biyan babban sakamako don kawai mu iya ganin gobe.

"Da fatan Allah ya ci gaba da ta'azantar da danginku."

KU KARANTA: Bayan Amincewa Fulani Makiyaya Su Dawo Kano, 'Yan Sanda Sun Ba Da Sharadi

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Farouk Yahaya a matsayin shugaban dakarun sojin kasa na Najeriya.

Yahaya, mai mukamin manjo janar zai maye gurbin marigayi Attahiru Ibrahim a take.

Kafin nadinsa, Yahaya shine babban kwamandan Div 1 na rundunar sojin kasa ta Najeriya.

Kamar yadda hedkwatar dakarun sojin kasa ta Najeriya ta wallafa a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Manjo Janar Farouk Yahaya a matsayin sabon shugaban sojin kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel