Zan Bulale Babangida Aliyu: Gwamna Wike Ya Yi Barazanar Zane Tsohon Gwamnan Neja
- Gwamnan jihar Ribas ya yi barazanar zane tsohon gwamnan jihar Neja Babangida Aliyu
- A wani bidiyon da ya yadu a kafar Tuwita, an ga sadda gwamna Wike ke cin alwashin zane Aliyu
- Ya kuma bayyana cewa, yana mamakin meye yasa har yanzu PDP ba ta kore shi saboda wasu dalilai
Nyesom Wike, gwamnan jihar Ribas, ya ce zai yiwa Babangida Aliyu, tsohon gwamnan jihar Neja bulala.
An ga Wike yana barazanar bulale tsohon gwamnan a cikin wani faifan bidiyo wanda ya yadu a shafukan sada zumunta, musamman Tuwita.
Gwamnan na Ribas yana mayar da martani ne ga maganganun da aka ta'allaka ga Aliyu.
A watan Afrilu, Aliyu ya ce gwamnonin arewa sun ki yi wa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan aiki a zaben 2015 saboda ya bijirewa yarjejeniyar da suka yi cewa ba zai sake neman wani wa’adin ba.
KU KARANTA: Bayan Amincewa Fulani Makiyaya Su Dawo Kano, 'Yan Sanda Sun Ba Da Sharadi
Amma da yake magana a ranar Litinin a gidan gwamnati a Port Harcourt, babban birnin jihar Ribas, Wike ya ce abin takaici ne cewa har yanzu PDP ta bar tsohon gwamnan a matsayin mambanta.
Wike ya ce "Aliyu yana ganin a wancan lokacin ne suke motsawa ko'ina, suna cewa suna yakar [PDP]".
“Da mun yi masa bulala matuka. Jihar Ribas ba haka bane… Zan yi masa bulala a nan.”
Kalli bidiyon da yake barazanar:
KU KARANTA: An Gano Gawarwaki 13 Cikin Mutane 200 da Jirgi Ya Kife Dasu a Kebbi
A wani labarin, Rauf Aregbesola, ministan cikin gida, ya ce yana cikin "gungun 'yan siyasa masu himma da taka-tsantsan" wadanda ba za su yi tsalle kawai su shiga takarar shugabancin kasa a 2023 ba tare da yin la'akari da kyau ba.
Aregbesola ya bayyana hakan ne a ranar Talata a wani taron tattaunawa mai taken: "Afirka: Bijiro da Tambayoyi kan Shugabanci".
Ministan, lokacin da wani da ya halarci taron ya tambaye shi ko yana da shirin tsayawa takarar kujerar shugaban kasa a 2023, cewa ya yi ba shi da amsa ga tambayar, TheCable ta ruwaito.
Asali: Legit.ng