Rundunar Yan Sanda Ta Fatattaki Yan Bindiga Daga Kai Hari, Ta Sheƙe 4 a Jihar Katsina

Rundunar Yan Sanda Ta Fatattaki Yan Bindiga Daga Kai Hari, Ta Sheƙe 4 a Jihar Katsina

- Rundunar yan sanda ta bayyana cewa ta samu nasarar hana wasu yan bindiga kai hari Ƙauyen Dangeza jihar Katsina

- Kakakin rundunar na jihar Katsina, SP Gambo Isa, shine ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar

- Yace jami'an yan sanda sun yi artabu da maharan, kuma sun kashe mutum huɗu daga cikin su

Rundunar yan sanda ta kori yan bindiga yayin da suka kai hari ƙauyen Dangeza, ƙaramar hukumar Batsari a jihar Katsina, kamar yadda daily nigerian ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Tsohon Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Ya Sauya Sheƙa Zuwa Jam’iyyar PDP

Wannan na ƙunshe ne a cikin wani jawabi da kakakin rundunar jihar, SP Gambo Isa, ya fitar a jihar Katsina, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Yace: "Ranar Laraba da misalin ƙarfe 4:30 na yamma, DPO na Batsari ya jagoranci tawagar jami'an yan sanda zuwa ƙauyen Dangeza, suka fatattaki wasu yan bindiga da suka yi ƙoƙarin kai hari ga mazauna garin."

Rundunar Yan Sanda Ta Fatattaki Yan Bindiga Daga Kai Hari, Ta Sheƙe 4 a Jihar Katsina
Rundunar Yan Sanda Ta Fatattaki Yan Bindiga Daga Kai Hari, Ta Sheƙe 4 a Jihar Katsina Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

"Tawagar jami'an sun yi musayar wuta da yan bindigan, amma iya yaƙi da dabarun yaƙin da jami'an yan sandan suka yi amfani dashi yasa maharan tserewa zuwa cikin daji tare da munanan raunukan harbi da a jikinsu."

"Bayan kammala artabun, an gano gawarwakin yan bindiga huɗu, tare da mashinan hawa uku."

KARANTA ANAN: Mun Cafke Duk Wani Mai Hannu a Harin da Aka Kaiwa Gwamnan Benuwai, IGP

Mr. Isa ya roƙi mutane da su cigaba da baiwa hukumomin tsaro haɗin kai, kuma su rinƙa kai musu rahoton ayyukan yan bindiga.

Hakanan kakakin yan sandan ya roƙi mutane su cigaba da tona asirin yan ta'adda, musamman waɗan da ke kai musu makamai zuwa cikin daji.

A wani labarin kuma Sojoji a Ƙasar Mali Sun Saki Hamɓararren Shugaban Ƙasar da Firaminista

Sojoji a ƙasar Mali sun saki shugaban ƙasa da Firaminista, waɗanda aka yi wa juyin mulki a ƙasar.

Rahotanni daga ƙasar sun bayyana cewa an sako shugabannin biyu ne da tsakar daren ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel