Da Ɗumi-Ɗumi: Sojoji a Ƙasar Mali Sun Saki Hamɓararren Shugaban Ƙasar da Firaminista

Da Ɗumi-Ɗumi: Sojoji a Ƙasar Mali Sun Saki Hamɓararren Shugaban Ƙasar da Firaminista

- Sojoji a ƙasar Mali sun saki shugaban ƙasa da Firaminista, waɗanda aka yi wa juyin mulki a ƙasar

- Rahotanni daga ƙasar sun bayyana cewa an sako shugabannin biyu ne da tsakar daren ranar Alhamis

- Wannan shine juyin mulki na biyu da sojojin suka jagoranta a Mali cikin watanni tara

Sojojin da suka jagoranci juyin mulki a ƙasar Mali sun saki hamɓararren shugaban ƙasar, Bah Ndaw, da Firaminista, Moctar Ouane,.kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Tawagar Goodluck Jonathan Ta Gana da Shugaban Ƙasar Mali da Aka Hamɓarar

Rahoton da BBC ta ruwaito ya nuna cewa an saki shuwagabannin biyu ne da misalin ƙarfe 1:00 na daren ranar Alhamis 27 ga watan Mayu.

Da Ɗumi-Ɗumi: Sojoji a Ƙasar Mali Sun Saki Hamɓararren Shugaban Ƙasar da Firaminista
Da Ɗumi-Ɗumi: Sojoji a Ƙasar Mali Sun Saki Hamɓararren Shugaban Ƙasar da Firaminista Hoto: @bbchausa
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Shugaba Buhari Ya Sake Taɓo Hanyar Magance Matsalar Tsaro, Yace Yana Buƙatar Haɗin Kan Yan Najeriya

Sojojin sun tsare shugaban ƙasar da Firaminista tun ranar Litinin data gabata a sansanin su.

Hakanan kuma bayan tsare su da sojin suka yi, sun tilasta musu yin murabus daga kan muƙaman su.

Legit.ng hausa ta kawo muku rahoto cewa a jiya tawagar ƙungiyar kasashen nahiyar Africa ECOWAS ta gana da shugaban ƙasar da Firamininsta.

Tawagar wakilan ƙarƙashin jagorancin Dr. Goodluck Ebele Jonathan, tsohon shugaban ƙasar Najeriya ta gana da shugaban ne biyo bayan hamɓarar da shi da sojoji suka yi ranar Litinin.

Wannan shine karo na biyu da sojoji a ƙasar Mali suka yi juyin mulki a ƙasar cikin watannin da ba su wuce tara ba.

A wani labarin kuma Ya Kamata a Baiwa Jihohi Damar Yanke Kananan Hukumomi Nawa Zasu Iya Ɗauka, El-Rufa'i

Gwamna Malam Nasiru El-Rufa'i, yace kamata yayi a baiwa gwamnonin jihohi damar yanke yawan kananan hukumomin da zasu iya ɗauka.

Gwamnan yace idan akace za'a maƙala wa gwamnatin tarayya dukka ƙananan hukumomin ƙasar nan to an saɓawa tsarin mulkin jamhuriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel