Da Ɗumi-Ɗumi: Tsohon Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Ya Sauya Sheƙa Zuwa Jam’iyyar PDP

Da Ɗumi-Ɗumi: Tsohon Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Ya Sauya Sheƙa Zuwa Jam’iyyar PDP

- Jam'iyyar PDP tayi babban kamu yayin da tsohon gwamnan jihar Cross Rivers, Donald Duke, ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar

- An tabbatar da komwar Mr. Duke zuwa jam'iyyar PDP ne yau Laraba, bayan ɗaukar kwanaki ana yaɗa jita-jita

- Wannan na zuwa ne biyo bayan sauya sheƙar gwamnan jihar Cross Rivers, Ben Ayade, zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

Donald Duke, tsohon gwamnan jihar Cross Rivers ya sauya sheƙa zuwa babbar jam'iyyar Adawa PDP, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Sojoji a Ƙasar Mali Sun Saki Hamɓararren Shugaban Ƙasar da Firaminista

Jaridar ta ruwaito cewa shugaban kwamitin riƙo na jam'iyyar PDP a yankin kudu maso kudancin ƙasar nan, Effiok Cobham, shine ya bayyana haka ranar Laraba 26 ga watan Mayu.

Da aka tambayeshi akan raɗe-radin da ake cewa tsohon gwamnan ya dawo PDP, Mr. Cobham yace: "Eh, harma yayi rijista da jam'iyya."

Da Ɗumi-Ɗumi: Tsohon Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Ya Sauya Sheƙa Zuwa Jam’iyyar PDP
Da Ɗumi-Ɗumi: Tsohon Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Ya Sauya Sheƙa Zuwa Jam’iyyar PDP Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Legit.ng ta gano cewa, Duke ɗan asalin jam'iyyar PDP ne kafin ya fice a shekarar 2018 yakoma SDP, inda aka tsayar dashi takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2019.

Mr. Duke ya riƙe muƙamin gwamnan jihar Cross Rivers na tsawon zango biyu daga Shekarar 1999 zuwa 2007.

Wannan na zuwa ne bayan gwamnan jihar Cross Rivers, Ben Ayade, ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC.

KARANTA ANAN: Shugaba Buhari Ya Sake Taɓo Hanyar Magance Matsalar Tsaro, Yace Yana Buƙatar Haɗin Kan Yan Najeriya

Gwamnan ya bada wannan sanarwar ne ranar Alhamis 20 ga watan Mayu, lokacin taron sa da wasu gwamnonin APC waɗanda suka kai masa ziyara a gidan Gwamnatin jihar.

Yayin da yake bada sanarwar ficewa daga PDP zuwa APC, gwamna Ayade yace wannan matakin da ya ɗauka zaisa jihar Cross Rivers ta samu ayyuka da dama daga gwamnatin tarayya.

A wani labarin kuma Mun Cafke Duk Wani Mai Hannu a Harin da Aka Kaiwa Gwamnan Benuwai, IGP

Rundunar yan sanda ta bayyana cewa ta kama dukkan masu hannu a harin da aka kaiwa gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom.

Muƙaddashin sufetan yan sanda na ƙasa, Usman Baba, Shine ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel