Mun Cafke Duk Wani Mai Hannu a Harin da Aka Kaiwa Gwamnan Benuwai, IGP

Mun Cafke Duk Wani Mai Hannu a Harin da Aka Kaiwa Gwamnan Benuwai, IGP

- Rundunar yan sanda ta bayyana cewa ta kama dukkan masu hannu a harin da aka kaiwa gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom

- Muƙaddashin sufetan yan sanda na ƙasa, Usman Baba, Shine ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja

- Yace har yanzun suna tsare ba tare da an gurfanar da su gaban kotu ba saboda yajin aikin da ma'aikatan kotu ke yi

Rundunar yan sanda ta sanar da cewa ta cafke mutum 10 da take zargi suna da hannu a harin da aka kaiwa gwamnan Benuwai, Samuel Ortom, kamar yadda Premium times ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Sojoji a Ƙasar Mali Sun Saki Hamɓararren Shugaban Ƙasar da Firaminista

Muƙaddashin Sufeto janar na yan Sanda (IGP), Usman Alƙali, shine ya sanar da haka Ranar Alhamis a taron Manema labarai, Abuja, kamar yadda guardian ta ruwaito.

"Waɗanda suka kitsa da waɗanda suka kai harin duk mun damƙe su, kuma muna cigaba da gudanar da bincike," inji shi

Mun Cafke Duk Wani Mai Hannu a Harin da Aka Kaiwa Gwamnan Benuwai, IGP
Mun Cafke Duk Wani Mai Hannu a Harin da Aka Kaiwa Gwamnan Benuwai, IGP Hoto: @OrtomSamuel
Asali: Facebook

.Sufetan yace sakamakon binciken da suka yi zuwa yanzun yasha banban da ikirarin da gwamnan yayi.

Bayan kai masa harin, Gwamna Ortom ya bayyana cewa wasu yan bindiga da yake zargin fulani makiyaya ne sun kai masa hari a gonar sa dake kusa da Tyo-mu, kan hanyar Makurdi-Gboko, jihar Benuwai.

KARANTA ANAN: Shugaba Buhari Ya Sake Taɓo Hanyar Magance Matsalar Tsaro, Yace Yana Buƙatar Haɗin Kan Yan Najeriya

Sufetan yan sandan yace har yanzun waɗanda aka kama ɗin suna tsare a wurin jami'an yan sanda ba tare da an gurfanar da su ba saboda ma'aikatan kotu na yajin aiki.

"Muna tsare da su sama da wata ɗaya nan baya saboda kotu a kulle take tun tsawon watanni uku da suka shuɗe, ina zamu kai su?" inji IGP.

A wani labarin kuma Tawagar Goodluck Jonathan Ta Gana da Shugaban Ƙasar Mali da Aka Hamɓarar

Tawagar wakilan ƙungiyar kasashen nahiyar Afirka ECOWAS ta gana da hamɓararren shugaban Mali da Firaminista.

Shugaban Mali da Firaminista sun shaida wa wakilan ECOWAS ɗin sun yi murabus daga kan muƙamansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel