Taɓarɓarewar Tsaro: CUPP Ta Buƙaci Shugaba Buhari Yayi Murabus
- Haɗakar jam'iyyun siyasa CUPP, sun yi kira ga shugaban ƙasa Buhari yayi murabus daga kujerar domin gwamnatinsa ta gaza
- Shugaban kwamitin yaɗa labarai na CUPP, Chukwudi Ezeobika, shine ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar a Abuja
- CUPP sunce Buhari ya gaza ta kowanne ɓangare kamar tsaro, lafiya, samar da wutar lantarki da dai sauransu
Haɗakar jam'iyyun siyasa CUPP, ta kira yi shugaban ƙasa Buhari da yayi murabus daga kujerarsa saboda ya gaza wajen daƙile matsalar tsaron dake ƙara taɓarɓarewa a Najeriya, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Babu Wani Makami da Zai Yi Nasara Kan Matsalar Tsaro Matuƙar Mutane Na Cikin Talauci, Sanatan APC
A wani jawabi da shugaban kwamitin yaɗa labarai na CUPP, Chukwudi Ezeobika, ya fitar, yace ya kamata Buhari yayi murabus saboda gazawar gwamnatinsa ta APC.
Wani sashin jawabin yace:
"Ƙaruwar ayyukan ta'addanci, satar mutane, rikici tsakanin makiyaya da manoma da dukkan sauran matsalolin tsaro suna nuna cewa gwamnatin Buhari ba zata iya kare rayuwar yan Najeriya da dukiyoyin su ba."
KARANTA ANAN: Jami'an Tsaro Sun Cafke Yan Bindiga 37 Dake Shirin Kai Hari INEC da Ofshin Yan Sanda
"Gurɓata ɓangarori masu muhimmanci ga rayuwar ɗan Najeriya kamar, tsaro, lafiya, samar da hasken wutar lantarki, tattalin arziƙi da sauransu ya sanya wajibi ne shugaba Buhari yayi murabus daga kujerarsa."
"Yawan kiraye-kirayen ɓallewa daga ƙasa da ake samu daga ɓangarori daban-daban na Najeriya, duk suna faruwa ne sakamakon nuna halin ko in kula da gwamnatin Buhari ke yi, kuma hakan barazana ce ga kasancewar Najeriya ƙasa guda ɗaya."
A wani labarin kuma Mutuwar COAS Ibrahim Attahiru Ya Ƙara Jefa Mu Cikin Matsaloli, inji Buhari
Shugaba Buhari yace mutuwar shugaban rundunar Soji da sauran jami'ai 10 ya ƙaro matsaloli a ƙasar nan, kamar yadda the cable ta ruwaito.
Shugaban yace Allah ne kaɗai yasan da faruwar wannan lamarin, amma ya faru a lokacin da ƙasar ke cikin ƙalubalen tsaro.
Asali: Legit.ng