Shugaba Kim Jong-un ya haramta saka ɗamammun wanduna da askin banza a kasarsa
- Shugaban kasa Kim Jong-un na kasar Korea ta arewa ya haramta saka damammun wanduna a kasar
- Baya ga hakan, ya hana saka fasassun wanduna, bulin hanci ko kunne, saka riguna masu take da sauransu ga matasan kasar
- Kasar ta haramta kallon fina-finan Korea ta kudu tare da sauraron wakokin wasu kasashe domin kiyaye al'adunsu
Shugaban kasan Korea ta arewa ya haramta saka damammun wanduna tare da askin banza a kasar sakamakon tsoron lalacewar tarbiyar matasa ta hanyar kwaikwayon kasashen yamma.
Hukuncin ya biyo baya ne sakamakon ganin cewa gayun zai iya janyo miyagun halayya a cikin matasan kasar, Britain Daily Express ta ruwaito.
"Dole ne mu ankare da kowacce alamar rayuwar 'yan jari hujja kuma dole mu yake su tare da kawar dasu," Rodong Sinmum, wani ma'aikaci kuma jigo a jam'iyya me mulki a kasar ya rubuta.
"Tarihi ya koyar damu cewa dole kasa ta kiyaye kada ta tarwatse tamkar bangon kasa duk da kuwa karfin tattalin arzikinta da tsaro. Dole ne mu rungumi yanayin rayuwarmu."
KU KARANTA: Hotunan ziyarar ta'aziyyar da Aisha Buhari ta kaiwa matar Janar Attahiru sun bayyana
Kamar yadda sabuwar dokar tace, ba za a bar 'yan kasar Korea ta arewa suna sanya damammun wanduna, fasassu, bulin hanci ko kunne, saka riguna masu take da sauransu, The Express ta ruwaito.
Askin banza da tura gashin kai duk abubuwa ne da kasar Korea ta arewa ba zasu lamunta ba.
A karkashin sabuwar dokar, mata da maza na kasar Korea ta arewa dole ne su yi aski cikin halastattun aski 15 da kasar ta amince dasu.
The Express ta ruwaito cewa, jami'an Pyongyang dake Korea ta arewa na son ganin bayan mawaka bayan nasarar da kungiyoyin K-pop irinsu BTS da Blackpink suka samu.
Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Yonhap ya sanar, a watan Disamba ne Korea ta arewa tace za ta tsananta hukunci ga duk wanda ta samu da bidiyoyin da aka yi a Korea ta kudu.
An saka dokar ne domin hana al'adun wasu kasashe baya da na kasar shigowa cikinsu balle su kwaikwaya.
KU KARANTA: 2006: Yadda hatsarin jirgin sama ya ritsa da sojoji masu mukamin janar 10 a Binuwai
A wani labari na daban, Dan majalisar wakilai, Abdulrazaq Namdaz, ya bada labarin yadda ya kusa shiga jirgin saman da yayi hatsari har ya kashe shugaban sojin kasa, Ibrahim Attahiru da wasu jami'ai 10.
Namdaz wanda ke shugabantar kwamitin al'amuran sojin kasa ya sanar da hakan a wata tattaunawa da yayi da Channels TV a ranar Lahadi, 23 ga watan Mayu.
Dan majalisar yace an gayyaceshi domin halartar yayen sojoji da za a yi a Zaria, jihar Kaduna. Ya ce da zai je kuwa babu shakka jirgin su Attahiru zai bi.
Asali: Legit.ng