Tankar Man Fetur Ta Fashe a Jihar Lagos, Mutane da Dama Sun Sha da Ƙyar

Tankar Man Fetur Ta Fashe a Jihar Lagos, Mutane da Dama Sun Sha da Ƙyar

- Wata tankar dakon man fetur ta faɗi sannan ta fashe da safiyar Talata a kan hanyar Ikotun dake yankin Alimosho jihar Lagos

- Lokacin da motar ke tangal-tangal bayan kasa shawo kanta da Direban yayi, mutanen dake wajen suka fara gudu domin tseratar da ransu

- Hukumar bada agaji ta jihar Lagos LASEMA ta samu nasarar kashe wutar tare da haɗin guiwar hukumar kashe gobara ta ƙasa

Mazauna yankin da matafiya sun sha da ƙyar yayin da wata tankar dake maƙare da man fetur ta fashe da sanyin safiyar yau Talata a Banire, kan hanyar Ikotun, yankin Alimosho jihar Lagos.

KARANTA ANAN: Shugaba Buhari: Mutuwar COAS Ibrahim Attahiru Ya Ƙara Jefa Mu Cikin Matsaloli

A cewar wata majiya lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:00 na dare, kamar yadda Vangurad ta ruwaito.

Tankar Man Fetur Ta Fashe a Jihar Lagos, Mutane da Dama Sun Sha da Ƙyar
Tankar Man Fetur Ta Fashe a Jihar Lagos, Mutane da Dama Sun Sha da Ƙyar Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Babu wanda ya rasa ransa ko waɗan da suka ji rauni, kuma ba'a yi asarar dukiyoyi ba a lokacin da wutar ke ci saboda mutanen dake wajen sun yi gudun tsira da rayuwarsu, Kamar yadda the nation ta ruwaito.

Ɗaya daga cikin waɗan da suka shaida lamarin da idon su, Mallam Audu Hassan, ya bayyana cewa direban motar yana cikin gudu mai tsanani lokacin da hatsarin ya faru.

Yace: "Ban yi barci ba lokacin da naji ƙarar wata mota mai matsanancin gudu, Na ga wata tankar mai direban na ƙoƙarin shawo kanta, ba zato sai motar ta fadi mutanen wajen suka fara gudu don tsira da rayuwarsu."

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Wasu Yan Bindiga Sun Sake Bankawa Ofishin INEC Wuta a Enugu

Darakta janar na hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Lagos LASEMA, Dr. Olufemi Oke-Osanyintolu, ya tabbatar da faruwar lamarin amma yace sun shawo kan komai.

Osanyintolu yace: "Lokacin da muka iso wajen mun fahince cewa wata tanka maƙare da man fetur ce da aka kasa shawo kanta ta faɗi a gefen hanya, wanda hakan yasa ta fashe kuma wuta ta ɓarke."

"Babu wanda ya mutu ko yaji rauni kuma babu wata dukiya da aka rasa, sashin kashe wuta na hukumar mu tare da hukumar kashe wuta ta ƙasa sun samu nasarar kashe wutar baki ɗaya."

A wani labarin kuma Kwamishinan Sokoto, Tureta, Ya Rigamu Gidan Gaskiya Bayan Shafe Shekara 14 a Ofis

Kwamishinan Noma a jihar Sokoto, Alhaji Arziƙa Tureta, ya rigamu gidan gaskiya bayan fama da rashin lafiya.

Tureta ya riƙe muƙamin kwamishina tun zamanin mulkin tsohon gwamnan Sokoto, Aliyu Wamako.

Asali: Legit.ng

Online view pixel