Gwamna Wike ya bugi kirji ya bayyana abunda zai faru da PDP idan ya fice
- Gwamna Nyesom Wike yayi alfahari game da mahimmancin sa a jam'iyyar adawa ta PDP
- Fitaccen gwamnan jihar ta Ribas ya bayyana kansa a matsayin kadara ga jam’iyyar siyasar
- Wike ya kuma caccaki wasu mambobin kwamitin aiki na jam’iyyar ta kasa
Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike a ranar Litinin, 24 ga watan Mayu, ya ce idan ya fice daga jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) jam’iyyar siyasar za ta wahala.
Daily Trust ta rahoto cewa Wike yayi wannan magana ne kasa da mako guda bayan Gwamna Ben Ayade ya sauya sheka zuwa APC.
KU KARANTA KUMA: Buhari ya dage taron majalisar zartarwa, yana makokin Attahiru da sauran jami'an soji
Gwamnan yayin ganawa da manema labarai a gidan gwamnati, a Fatakwal, ya yi alfahari game da abin da jam'iyyar adawa za ta fuskanta idan ya yanke shawarar barin cikinta.
Yayin da yake bayyana kansa a matsayin kadara ga PDP, Wike ya caccaki wasu mambobin Kwamitin Ayyuka na jam’iyyar ta kasa.
Ya bayyana su a matsayin masu karɓar haraji kuma ya ci gaba da cewa yana nan a kan maganarsa.
KU KARANTA KUMA: Badakala: Majalisa Na Neman Akanta-Janar, Da Sauransu Kan Gibi a Kudaden da Aka Kwato
Jaridar Daily Post ta kawo cewa gwamnan ya jadadda cewa ba wai dukka yan kwamitin NWC bane masu karbar haraji illa wasun su.
A gefe guda, mataimakin gwamnan ya dauki wannan mataki ne kwanaki hudu bayan mai gidansa, gwamnan jihar Kuros Riba, Ben Ayade, ya fice daga jam’iyyar PDP.
Da wannan mataki da Farfesa Ivara Ejemot Esu ya dauka a jiya, ya kawo karshen rade-radin cewa shi da mai gidansa ba su tafiya a kan shafi guda na siyasa.
A wani bidiyo da Channels TV ta wallafa, ta tabbata cewa Ivara Esu yayi ban kwana da jam’iyyar PDP da ta ba su nasarar lashe zabe a 2015 da kuma 2019.
Asali: Legit.ng