Ahmed Musa na shirin barin Kano Pillars a watan Yuni, ya yi jinjina ta musamman ga Ali Rabiu
- Ga dukkan alamu Kaftin din Super Eagles, Ahmed Musa na iya barin kungiyar Kano Pillars a watan Yuni
- Musa ne ya yi tsokacin hakan a wata hira da aka yi da shi, sai dai kuma bai bayyana inda zai je ba a nan gaba
- Ya kuma jinjina wa takwaransa, Rabiu Ali saboda karrama shi da ya yi ta hanyar mika masa mukamin kaftin din Kano Pillars
Kaftin din Super Eagles, Ahmed Musa ya yaba wa takwaransa, Rabiu Ali saboda karrama shi da ya yi ta hanyar mika masa mukamin kaftin din Kano Pillars.
'Yan sakanni kaɗan kafin karawar Kano Pillars wasan mako na 21 da Adamawa United a ranar Lahadin da ta gabata, Ali ya mika madaurin hannu na kaftin ɗin ga Musa wanda a ƙarshe ya sa ƙungiyar ta yi nasara da 1-0.
KU KARANTA KUMA: Hoton jarumin Kannywood Ali Nuhu tare da kyawawan yaransa
A wata hira da aka yi da shi jiya, Musa wanda ya bayyana Rabiu Ali a matsayin fitaccen dan wasan Kano Pillars ya ce har zuciyarsa ya ji girmamawa da irin wannan karimcin na dan wasan wanda aka fi sani da ‘Pele’, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Ya ce “Ina matukar girmama Rabiu Ali. Yana ɗaya daga cikin kwaraza na. Na yi wasa tare da shi a lokutan baya a Kano Pillars.
“Kuma dawo da wasa da shi, ina matukar girmama shi sosai kuma ina so in yi masa babban godiya kan abin da ya aikata kwanakin baya.
“Ba kowa bane zai iya yin hakan. Ina matukar son na gode masa.”
KU KARANTA KUMA: Fitaccen gwamnan PDP na gab da komawa APC yayinda takwarorinsa 7 daga jam’iyya mai mulki suka dira a jihar
A halin yanzu, tsohon dan wasan gaba na CSKA Moscow da kuma Leicester City ya ba da bayanin cewa zai iya barin Kano Pillars a watan Yuni.
Kodayake ya ki bayyana inda zai je nan gaba, ya ce zuwa wata mai zuwa, za a san hakan.
A baya Legit.ng ta kawo cewa kaftin din Super Eagles Ahmed Musa na shirin komawa kungiyar kwallon kafa ta West Bromwich Albion masu buga Premier a kan yarjejeniyar wani gajeren lokaci.
Dan wasan mai shekaru 28 bai kasance a wata kungiyar kwallon kafa ba tun lokacin da ya bar Al Nassr a cikin Oktoba 2020, The Punch ta ruwaito.
A cewar Daily Mail, Baggies sun nemi bizar dan wasan kuma sun shirya don duba lafiyarshi a ranar Laraba.
Asali: Legit.ng