Fitaccen gwamnan PDP na gab da komawa APC yayinda takwarorinsa 7 daga jam’iyya mai mulki suka dira a jihar

Fitaccen gwamnan PDP na gab da komawa APC yayinda takwarorinsa 7 daga jam’iyya mai mulki suka dira a jihar

- Rahotanni sun ce wasu gwamnonin APC sun isa Calabar yayin da suke kara kaimi wajen jan hankalin Gwamna Ayade zuwa jam’iyya mai mulki

- An shirya gwamnonin za su gana da gwamnan jihar Cross River a safiyar ranar Alhamis, 20 ga watan Mayu

- Ba a bayyana ko gwamna Ayade zai saurare su ya koma APC ba ko kuma ya ci gaba da zama a PDP

Wasu gwamnoni a karkashin jam'iyyar All Progressive Congress (APC) a yammacin ranar Laraba, 19 ga Mayu, sun isa Calabar don shawo kan Gwamna Ben Ayade ya fice daga Peoples Democratic Party (PDP).

Jaridar The Nation ta bada rahoton cewa tawagar ta APC ta samu jagorancin gwamnan Yobe Mai Mala Buni, wanda kuma shine shugaban kwamitin riko na kasa na APC.

KU KARANTA KUMA: Jerin jihohin da aka kona ofishoshin INEC cikin watanni 24

Fitaccen gwamnan PDP na gab da komawa APC yayinda takwarorinsa 7 daga jam’iyya mai mulki suka dira a jihar
Fitaccen gwamnan PDP na gab da komawa APC yayinda takwarorinsa 7 daga jam’iyya mai mulki suka dira a jihar Hoto: NurPhoto
Asali: Getty Images

Legit.ng ta tattaro cewa Buni ya isa Calabar ne a yammacin ranar Laraba don haduwa da takwaran sa na Imo, Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo wanda ya kasance a kasa.

An tattaro cewa ana sa ran gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahai da wasu gwamnonin APC za su isa jihar.

A cikin rahoton ta, Daily Sun ta bayyana cewa ana sa ran gwamnonin APC bakwai za su gana da Ayade a safiyar ranar Alhamis, 20 ga watan Mayu, sannan ta kara da cewa wadanda suka fito daga jihohin Ekiti, Plateau, da Yobe suma sun isa Calabar.

KU KARANTA KUMA: A karon farko: ’Yan bindiga sun kai hari cikin garin Batsari da ke Katsina

Jaridar ta kuma ambaci wasu majiyoyi suna cewa gwamnonin sun je jihar ne domin lallashin Ayade ya koma APC saboda rikicin da ya dabaibaye PDP a jihar.

Sai dai, an ambaci wata majiyar da ke nuna cewa Gwamna Ayade ba zai sauya sheka zuwa APC ba duk rintsi amma zai saurari sanin abin da suke da shi ga jihar.

Ayade da wasu mambobin majalisar kasa da shugabannin PDP sun yi ta fafatawa a kan mamayar tsarin jam’iyyar da kujerar sanata ta arewa.

Wannan ya haifar da rikicin cikin gida a jam'iyyar PDP reshen jihar Cross River.

Legit.ng ta lura cewa ziyarar gwamnonin APC na zuwa ne kusan makonni biyu bayan wasu gwamnonin PDP sun yi wani taro a jihar Cross River don dakatar da sauya shekar da Gwamna Ayade ke shirin yi.

Tawagar ta PDP ta kasance karkashin jagorancin shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar, gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal.

Tambuwal ya samu rakiyar gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, da takwaransa na jihar Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi.

A wani labarin, shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan, a ranar Laraba, 19 ga watan Mayu, ya ba da sanarwar dakatar da zaman majalisar na tsawon kwanaki bakwai masu zuwa.

Da yake magana a ranar Laraba a majalisar dattijan, Lawan ya bayyana cewa makon za a sadaukar da shi ne don sauraren taron yanki kan nazarin kundin tsarin mulki na 1999, jaridun Vanguard da The Nation suka ruwaito.

Shugaban Majalisar Dattawan ya ce: "Za mu dukufa ga aikin sake duba kundin tsarin mulki a makon gaba daya."

Asali: Legit.ng

Online view pixel