Hoton jarumin Kannywood Ali Nuhu tare da kyawawan yaransa

Hoton jarumin Kannywood Ali Nuhu tare da kyawawan yaransa

- Shahararren dan wasan kwaikwayo na Najeriya, Ali Nuhu, ya kasance uba mai alfahari da kyawawan 'ya'ya

- Dukkansu sun taru don daukar hoto bayan yaran nasa da na jaruma Hafsat Idris sun kai masa ziyara a ofishinsa

- Masu amfani da yanar gizo sun yaba da hoton tare da yi wa iyalan fatan alheri

Shahararren tauraron fina-finan Najeriya, Ali Nuhu, ya wallafa wani kyakkyawan hoto na zumunci inda aka gano shi tare da yaransa da na abokiyar aikinsa, Hafsat Idris.

Jarumin na Kannywood ya je shafinsa na Instagram domin wallafa hoton wanda ke nuni ga ziyarar da yaran suka kai masa a ofishinsa.

Ali ya zauna a kan tebur sannan ya kasance kewaye da yaransa Ahmed da Fatima da kuma sauran yaran abokiyar sana’ar tasa wato Muhammad, Hawaa da kuma Ramlah.

KU KARANTA KUMA: Fitaccen gwamnan PDP na gab da komawa APC yayinda takwarorinsa 7 daga jam’iyya mai mulki suka dira a jihar

Hoton jarumin Kannywood Ali Nuhu tare da kyawawan yaransa
Hoton jarumin Kannywood Ali Nuhu tare da kyawawan yaransa Hoto: @realalinuhu
Asali: Instagram

A cikin rubutun, tauraron fim din ya godewa yaransa da suka ziyarce shi.

Ya rubuta:

"Na gode da Ziyarar Yarana"

KU KARANTA KUMA: Jerin jihohin da aka kona ofishoshin INEC cikin watanni 24

Kalli kyakkyawan hoton iyalin a kasa:

Masoya da abokan aikin ɗan wasan sun ɗje ɓangaren sharhi don yaba kyakkyawan hoton. Karanta wasu daga cikin sharhinsu a kasa:

official_hafsaidris20

"So Masha Allah the king Allah ya bar zumici Ameen ❤️❤️❤️"

manlike._.yusuf

"Allah Ya kare wannan iyali"

Abdullahia_mai_gree:

"Madalla daddy muna zuwa"

Kingzeedabdul:

"Kyakkyawan iyali"

A wani labari, Ummi Ibrahim, fitacciyar tsohuwar jarumar Kannywood wacce aka fi sani da Ummi Zee Zee, ta tabbatar da rade-radin da ke cewa ta yi soyayya da Shugaban kasa a mulkin Soja, Ibrahim Babangida (IBB).

Akwai rahotanni a shafukan sada zumunta da ke cewa jarumar tana soyayya da tsohon Shugaban Kasar.

A cikin zantawa da Mujallar Daily Trust ta karshen mako, Zee Zee ta ce ta rabu da IBB.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel