A karon farko: ’Yan bindiga sun kai hari cikin garin Batsari da ke Katsina

A karon farko: ’Yan bindiga sun kai hari cikin garin Batsari da ke Katsina

- 'Yan bindiga sun kai hari garin Batsari da ke jihar Katsina inda suka kashe mutum daya

- Har ila yau maharan sun yi garkuwa da wasu mutane da dama a a harin wanda ya wakana a tsakar daren ranar Laraba

- Wannan shine karo na farko da suke kaddamar da hari a ainahin garin Batsari domin a kauyuka suke kai hare-haren baya

Wani rahoton jaridar Aminiya ya nuna cewa ’yan bindiga sun kai farmaki garin Batsari da ke Jihar Katsina a karo na farko, inda suka kashe mutum guda sannan suka kuma yi garkuwa da wasu da dama.

Jaridar ta ruwaito cewa wani mazaunin ya yankin ya shaida mata a wayar tarho cewa mutumin da aka kashe ya kasance manomi mai suna Iliya Bakon-Zabo.

KU KARANTA KUMA: Jerin jihohin da aka kona ofishoshin INEC cikin watanni 24

A karon farko: ’Yan bindiga sun kai hari arin Batsari da ke Katsina
A karon farko: ’Yan bindiga sun kai hari arin Batsari da ke Katsina Hoto: @PremiumTimesng
Asali: UGC

Ya ce: “Dazu, wata mata ta dawo, don haka ba za mu iya cewa ko duk wadanda suka bace suna hannunsu a yanzu ba ko a’a, amma a halin yanzu mun kirga mutum 27 da ba mu san inda suke ba.”

Majiyar ta kara da cewa maharan sun shiga garin Batsarin ne da misalin karfe 12.10 na talatainin daren Laraba, sannan suka fara harbi babu kakkautawa.

An tattaro cewa wannan shine karo na farko da ’yan bindigar suka shiga garin Batsari sakamakon duk hare-haren da suka gabata a Karamar Hukumar an kai su ne a kauyuka.

Sai dai majiyar ta ce jami’an tsaro sun yi nasarar tarwatsa ’yan bindigar, wanda a cewarta ba don kokarin da jami’an tsaro, da lamarin ya fi haka muni.

Kakakin ’yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya ce ’yan sanda da sojoji sun yi nasara fatattakar ’yan bindigar.

KU KARANTA KUMA: Majalisa na shirin kafa dokar daurin shekaru 15 ga duk wanda ya biya masu garkuwa kudin fansa

A wani labarin, Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da wani hari da miyagun 'yan bindiga suka kai karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna inda suka kashe mutum 8 tare da kone gine-gine a yankin.

Kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Laraba, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kamar yadda takardar tace, wadanda aka kashe a harin sun hada da: Samaila Gajere, Bawa Gajere, Bitrus Baba, Umaru Baba, Solomon Samaila, Sambo Kasuwa, Samaila Kasuwa da Gideon Bitrus.

Asali: Legit.ng

Online view pixel