Majalisa na shirin kafa dokar daurin shekaru 15 ga duk wanda ya biya masu garkuwa kudin fansa

Majalisa na shirin kafa dokar daurin shekaru 15 ga duk wanda ya biya masu garkuwa kudin fansa

- Yan majalisa na cigaba da neman mafita daga cikin lamarin garkuwa da mutane

- Masu satan mutane sun samu miliyoyin kudi daga fansa mutanen da suka sace

- Wannan abu ya zama ruwan dare a Najeriya musamman Arewa maso yamma

Majalisar dattawa a ranar Laraba ta gabatar da sabuwar dokar haramta biyan masu garkuwa da mutane kudin fansa.

Ezrel Tabiowo, hadimin shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan, a jawabin da ya saki ranar Laraba ya ce sabuwar dokar ta ketare mataki na biyu.

Ya kara da cewa Sanata Ezenwa Francis Onyewuchi ne ya gabatar da kudirin.

Dan majalisan ya bukaci a gyara dokar dakile ta'addanci an 2013 domin haramta biyan masu garkuwa da mutane kudin fansa don sakin wanda suka sace.

A cewar Onyewuchi, ya kamata a daure duk wanda ya biya masu garkuwa da mutane kudin fansa tsawon shekaru 15 a gidan gyara hali.

DUBA NAN: Nan da 2022 sabon kamfanin jirgin Nigeria Air zai fara aiki, Hadi Sirika

Majalisa na shirin kafa dokar daurin shekaru 15 ga duk wanda ya biya masu garkuwa kudin fansa
Majalisa na shirin kafa dokar daurin shekaru 15 ga duk wanda ya biya masu garkuwa kudin fansa Hoto: @NGRSenate
Asali: UGC

DUBA NAN: Ba zamu je Abuja sulhu da NLC ko FG ba idan ba'a dawo da lantarki ba, El-Rufa'i

Sabuwar dokar itace: "Duk wanda ya tura kudi, ko ya biya kudi, ko ya tattauna da masu garkuwa da mutane don sakin wani ya aikata laifi kuma za'a iya dauresa a kurkuku na tsawon shekaru 15."

Ya bayyana cewa dalilin haka shine garkuwa da mutane ya zama wani babban kasuwanci yanzu a Najeriya.

Ya bayyana cewa kasashe irinsu Amurka da Birtaniya basu yarda da biyan masu garkuwa da mutane kudin fansa ba.

"Biyan yan ta'adda kudin fansa haramun ne karkashin dokar Birtaniya 2000 yayinda Amurka ta yanke bata yarda da biyan kudin fansa ba," Onyewuchi ya kara.

A bangare guda, Gwamnatin tarayya ta gayyaci gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i, da shugabannin NLC zuwa wajen taron gaggawa data shirya domin yin sulhu a tsakanin su, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Gwamnatin ta sanya ranar Alhamis 20 ga watan Mayu domin tattaunawar sulhu tsakanin ɓangarorin biyu a babban Birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel