'Yan bindiga sun sheke mutum 8, sun kone coci da wasu gidaje a Kaduna
- Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da wani mugun hari da 'yan bindiga suka kai Chikun inda suka halaka rayuka 8
- Kamar yadda kwamishinan tsaron cikin gida na jihar ya sanar, 'yan bindigan sun bankawa wata coci da wasu gidaje wuta
- Mutanen da suka riga mu gidan gaskiya yayin wannan harin sun hada da: Samaila Gajere, Bawa Gajere, Bitrus Baba, Umaru Baba da sauransu
Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da wani hari da miyagun 'yan bindiga suka kai karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna inda suka kashe mutum 8 tare da kone gine-gine a yankin.
Kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Laraba, Daily Nigerian ta ruwaito.
Kamar yadda takardar tace, wadanda aka kashe a harin sun hada da: Samaila Gajere, Bawa Gajere, Bitrus Baba, Umaru Baba, Solomon Samaila, Sambo Kasuwa, Samaila Kasuwa da Gideon Bitrus.
KU KARANTA: Da duminsa: El-Rufai ya sha alwashin koran ma'aikatan da suka yi zanga-zanga da NLC
Aruwan ya kara da cewa ginin da aka kone mallakin cocin Assemblies of God ne tare da wasu gidajen dake da makwabtaka dasu.
A wani cigaba makamancin hakan, rundunar sojin ruwa dake zama a yankin Kujama sun halaka 'yan bindiga uku tare da damke wasu mutum biyu da ake zargin suna hada kai da 'yan bindigan tare da kai hari Wakwodna kusa da kauyen Kasso, karamar hukumar Chikun.
Kamar yadda Aruwan yace, dakarun dake Kujama sun yi gaggawar martani bayan rahoton harin da suka samu a kauyen Wakwodna kuma sun tura jami'ai da gaggawa, Vanguard ta ruwaito.
Ya kara da cewa 'yan bindigan sun tsere zuwa dajika bayan arba da dakarun inda suka bar shanun sata wadanda daga baya aka mika su ga masu su.
"Dakarun sun yi arangama da 'yan bindigan kafin kauyen Kaso kuma sun halaka uku daga cikin 'yan bindigan.
"Wasu mazauna yankin sun samu rauni yayin artabun kuma an kwashesu zuwa asibiti."
A yayin arangamar, dakarun sun damke wasu mutum biyu dake kaiwa 'yan bindigan bayanai masu suna Kapido Halilu da mai samar masu da kayayyaki Umar Maipashi.
KU KARANTA: Gwamna ya fatattaki kwamishinoni 25, shugaban ma'aikatansa da sakataren gwamnati
A wani labari na daban, 'yan bindiga sun yi garkuwa da alkali a cikin kotun Sharia dake kauyen Bauren Zakat a karamar hukumar Safana ta jihar Katsina.
Kamar yadda ganau suka sanar da Daily Trust, maharan sun balle kotun inda suka shiga wurin karfe 3 na yammacin ranar Talata kuma suka yi awon gaba da alkalin mai suna Alhaji Husaini Sama'ila.
An mayar da kotun shari'ar ne karamar hukumar Safana saboda dalilan tsaro. Har yanzu dai ba a san dalilin da ya kai alkalin kotu ba duk da yajin aikin da kungiyar ma'aikatan shari'a na Najeriya (JUSUN) ke ciki.
Asali: Legit.ng