Jerin jihohin da aka kona ofishoshin INEC cikin watanni 24
A wata hira da jaridar Daily Sun ta wallafa a ranar Asabar, 17 ga Afrilu, Sanata Enyinnaya Abaribe, shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dattawa, ya yi gargadin cewa babban zabe na 2023 ba zai iya faruwa ba idan ba a magance matsalar tsaro a kasar nan yadda ya kamata ba.
Duk da cewa da yawa na iya yin watsi da gargadinsa a matsayin bangaranci kawai, akwai wani ci gaba mai tayar da hankali a kasar wanda ke nuni da cewa makomar zaben 2023 na rawa a sama idan ba a yi wani abu mai tsauri ba da sauri.
A cikin watanni 24 da suka gabata, an samu wasu hare-hare da ake ganin an kai wa ofisoshin hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC a sassa daban-daban na kasar.
KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Shugaban majalisar dattawa ya dakatar da zaman zauren na kwanaki bakwai, ya bayar da dalilin
Hatta INEC ta nuna damuwarta game da tasirin wadannan hare-hare kan ayyukan zaben kasar, a cewar wata sanarwa daga kakakin INEC, Festus Okoye.
Legit.ng a wannan zaure ya zakulo ofisoshin INEC da aka kona cikin shekaru biyu da suka gabata.
1. jihar Abia
a. Ofishin INEC a karamar hukumar Aba ta kudu, jihar Abia
A ranar Lahadi, 13 ga watan Disamba an kina ofishin INEC a karamar hukumar Aba ta Kudu, a jihar Abia baki daya.
b. Ofishin karamar hukumar Arochukwu
A watan Oktoba na 2020, wasu 'yan iska sun lalata ofishin INEC a karamar hukumar Arochukwu da ke jihar Abia.
c. Ofishin INEC a karamar hukumar Ohafia
A daren Lahadi, 9 ga Mayu, 2021, an kone ofishin INEC da aka gyara kwanan nan a karamar hukumar Ohafia.
A cewar INEC, kusan ginin ya lalace. Baya ga kayan alatu, duk kayayyakin zabe da kayayyakin ofis sun lalace, majiyar Legit.ng ta tattaro.
KU KARANTA KUMA: Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar Ya Ce Ba Za Ayi Yaki Ba a Nigeria
2. jihar Akwa Ibom
Ofishin INEC a Essien Udim
A ranar Lahadi 2 ga watan Mayu ne wasu da ba a san ko su waye ba suka kona ofishin INEC a karamar hukumar Essien Udim.
Kwamishinan Zabe na Jihar (REC) Barr. Mike Igini ya tabbatar da faruwar lamarin.
3. FCT / Abuja
Wani bangare na ginin hukumar INEC da ke Abuja shima kwanan nan gobara ta kama.
Daraktan yada labarai da wayar da kan masu zabe na INEC, Oluwole Osaze-Uzzi, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Juma’a, 17 ga Afrilu, 2020.
Ya ce gobarar ta shafi ofishin daraktan zaben da sa ido kan jam’iyya a cikin ginin.
4. Jihar Ondo
A ranar Alhamis, 10 ga Satumba, 2020, kimanin makonni huɗu kafin zaɓen gwamnan jihar Ondo, kimanin na’urar card reader 5,141 be suka lalace a cikin wata gobara a babban ofishin hukumar na Akure, jihar Ondo.
5. jihar kano
Hakazalika, INEC ta sanar a ranar Litinin, 20 ga Afrilu, 2021, cewa cibiyoyin sarrafa bayanan ta da ke jihar Kano ta kama gobara.
6. Jihar Imo
A watan Fabrairun 2020, gobara ta babbake wani ofishin INEC a Orlu, jihar Imo, sakamakon konewar daji.
7. Jihar Anambra
Hakanan, a cikin watan Fabrairun 2020, ofishin INEC a karamar hukumar Idemili ta Arewa a jihar Anambra ta kama gobara.
8. Jihar Ribas
A shekarar 2019, wasu da ake zargin ‘yan bangar siyasa ne sun cinnawa ofishin INEC wuta a karamar hukumar Ngor Okpuala da ke jihar Imo.
Wadanda ake zargin ‘yan fashin ne sun shiga ofishin INEC ne lokacin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi da misalin karfe 2 na ranar Lahadi, 10 ga Maris, 2019, kafin su cinna wa ofishin wuta.
9. jihar Plateau
Jim kadan kafin zaben 2019, ofishin INEC da ke karamar hukumar Qua’an Pan a jihar Filato ya kone kurmus.
An ce gobarar ta afku ne daga wani jami’in tsaro da ya sha ya bugu.
10. Jihar Ebonyi
A shekarar 2019, ‘yan daba sun far wa ma’aikatan INEC a karamar hukumar Ezza ta arewa da ke jihar Ebonyi suka kwashe kayayyakin zabe da yawa.
‘Yan bangar sun mamaye ofishin rajistar INEC (RAC) da ke Okposi Umuoghara Community Secondary School da misalin karfe 2.15 na safiyar ranar 9 ga Maris, inda suka buge ma’aikatan tare da sace kayayyakin zaben.
Daga baya sun kona ginin makarantar firamare wanda ya kasance cibiyar rijista na INEC lokacin da suka gama da harin.
A wani labarin, hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce hare-haren da aka kai wa wasu ofisoshinta na kawo cikas ga shirye-shiryen babban zaben 2023.
A cikin makonnin da suka gabata, wasu ofisoshin INEC sun ga yawan hare-hare, abin da ya kai ga lalata wasu kayan aiki masu mahimmanci.
Da yake magana a kan ci gaban a cikin wata hira da Channels Television a ranar Litinin, Festus Okoye, mai magana da yawun INEC, ya ce hare-haren na yin mummunan tasiri kan ayyukan hukumar.
Asali: Legit.ng