Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar Ya Ce Ba Za Ayi Yaki Ba a Nigeria

Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar Ya Ce Ba Za Ayi Yaki Ba a Nigeria

- Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar III ya ce ba za a yi yaki ba a Nigeria

- Sarkin Musulmi ya yi wannan jawabin ne a ranar Laraba a Abuja wurin taron NIREC

- Ya bada shawarar a cigaba da zama ana tattauna ana sulhu domin hakan ne zai samar da zaman lafiya a kasar

Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma shugaban kwamitin koli ta harkokin musulunci, NSCIA, Alhaji Sa'ad Abubakar III ya ce ba za a yi yaki ba a Nigeria duk da kiraye-kirayen rabuwa da sassan kasar ke yi, Daily Trust ta ruwaito.

Ya furta hakan ne ranar Laraba a birnin tarayya Abuja yayin taron Kwamitin Addinai na Kasa, NIREC, da ake yi sau hudu a kowanne shekara.

Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar Ya Ce Ba Za Ayi Yaki Ba a Nigeria
Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar Ya Ce Ba Za Ayi Yaki Ba a Nigeria. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Dogo Gide Ya Kashe 12 Cikin Yaransa Kan Rikicin Rabon Kayan Sata a Niger

Sultan, wanda kuma shima shugaba ne daya daga cikin shugabannin NIREC ya ce ya yi imani da sulhu kamar yadda addinsa ta koyar da shi kuma zai yi amfani da sulhun da samar da zaman lafiya.

"Mutane suna da maganan yaki, ba za a yi yaki a Nigeria ba, wane zai yi yaki da wa?

"A gida daya, muna samun musulmi da kirista, akwai kabilu a kasarku, kunyi auratayya tsakanin ku.

"Don haka, duk hayanaiyar da mutane ke yi kawai ne domin su samu wani abu a kasar, idan ka dube su, tsiraru ne.

"A kasar nan, akwai mutane na gari da suke nufin talaka da alheri da sauran mutane kuma wannan shine abin da Allah ya hallice mu mu aikata," in ji Sultan.

Ya kara da cewa, "Don haka mu cigaba da aiki tare, mu cigaba da zama tare, mu cigaba da tattaunawa, Na yi imani da sulhu kuma babu abin da zai canja min zuciya ta domin addinin na ya koyar da sulhu kuma na yi imanin cewa babu abin da ya fi karfin a warware shi domin ko yaki ana yi ne domin a samar da zaman lafiya.

"Amma idan ka san za ka samar da zaman lafiya ba tare da yaki ba, mai zai saka ka dauki makamai? Zaman lafiya shine abu mafi muhimmanci ."

A wani rahoton daban kun ji cewa abin baƙin ciki ya faru a unguwar Alanamu da ke ƙaramar hukumar Ilorin ta Yamma a ranar Talata a lokacin da wani mutum Alhaji Taiye-Hassan Beki ya rasa ransa sakamakon gini da ya faɗo masa.

Daily Trust ta ruwaito cewa marigayin, Injiniyar lantarki mai yara huɗu yana fitsari ne a bayan gidansa lokacin ana ruwan sama sai wani sashi na ginin ya faɗo masa.

An dauki lokaci kafin a kai masa ɗauki domin ƴan uwansa ba su san abin da ya faru da shi ba a lokacin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel