INEC ta koka, ta ce babban zaben 2023 na iya samun matsala

INEC ta koka, ta ce babban zaben 2023 na iya samun matsala

- Lalata ofisoshin INEC na iya shafar shirye-shiryen babban zaben 2023 a cewar hukumar

- Ku tuna cewa wasu bata gari sun kona wasu ofisoshin INEC a wasu yankuna na kudu maso gabas da kudu maso kudu

- Da take ci gaba, hukumar ta ce wasu ma’aikatansu na rayuwa cikin tsoro

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce hare-haren da aka kai wa wasu ofisoshinta na kawo cikas ga shirye-shiryen babban zaben 2023.

A cikin makonnin da suka gabata, wasu ofisoshin INEC sun ga yawan hare-hare, abin da ya kai ga lalata wasu kayan aiki masu mahimmanci.

KU KARANTA KUMA: Matsalar Tsaro: CAN Ta Goyi Bayan Shawarar Tsohon Shugaban Ƙasa IBB, Tace Wannan Ba Shine Karon Farko Ba

INEC ta koka, ta ce babban zaben 2023 na iya samun matsala
INEC ta koka, ta ce babban zaben 2023 na iya samun matsala Hoto: Sodiq Adelakun
Asali: Original

Da yake magana a kan ci gaban a cikin wata hira da Channels Television a ranar Litinin, Festus Okoye, mai magana da yawun INEC, ya ce hare-haren na yin mummunan tasiri kan ayyukan hukumar.

Okoye ya lura cewa hukumar ta rasa kayan aiki masu mahimmanci da marasa mahimmanci, ciki harda janareto da na’urar card readers.

Ya yi bayanin cewa hukumar na iya samun hayar gidaje domin maye gurbin ofisoshin kananan hukumomin da aka kona, amma ya nuna damuwar cewa masu bayar da hayar wadannan gidaje ka iya shafar sakamakon zaben.

KU KARANTA KUMA: Fadar shugaban kasa ta bankado yunkurin sakin bayanan bogi kan lafiyar kwakwalwar Buhari

"Dangane da wasu daga cikin wadannan hare-haren da kuma abubuwan da suka haifar, ka sani a matakin kananan hukumomi, jami'an zabe suna aiki a matsayin manajan-daraktocin zabenmu," inji shi.

“Ba ma gudanar da zabe a babban ofishinmu na INEC. A matakin tushe ne ake gudanar da waɗannan zaɓukan. Hakanan kun san cewa mun gama tantancewa dangane da fadada damar masu jefa kuri'a a rumfunan zabe. A ofisoshin ƙananan hukumomi ne aka Tzara waɗannan. Sun shirya tsarin tsoffin mazabu da sabbin rumfunan zabe.

“Idan kuka afkawa ofisoshin kananan hukumominmu, to kuna harin iyawarmu da karfinmu na gudanar da zabe.

“Don haka, idan kuka lalata hukumar, illan yin hakan shi ne, wataƙila hukumar za ta je ta nemi gidan haya kuma lokacin da hukumar za ta je neman ofishin hayar, ba ka san halin siyasa da son zuciyar masu gidajen ba. Kuna iya fitowa kawai a ranar zaɓe ku gano cewa ofisoshinku suna kulle kuma babu cikakken abin da za ku yi game da hakan.

“Muna cikin fargabar cewa lamarin ya shafi shirye-shiryenmu. Hakanan mu ma muna cikin damuwa saboda wasu daga cikin jami'anmu yanzu suna rayuwa cikin tsoro dangane da abin da ke gudana.

"Ko shakka babu wannan abin da ke faruwa ba mai karbuwa bane, kuma zai karkatar da hankalin hukumar ne daga shirye-shiryen zaben 2023 da kuma na zabukan da muke shiryawa."

A wani labarin, Gwamnonin jam’iyyar PDP sun yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya aika da kudirin zartarwa ga majalisun dokokin kasa don yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulki ta yadda za a yi karin iko ga jihohi.

Kungiyar gwamnonin na PDP sun yi taro a Ibadan, babban birnin jihar Oyo a ranar Litinin don tattaunawa kan halin da kasa ke ciki, matsalar rashin tsaro, da tattalin arziki, The Cable ta ruwaito.

A karshen taron, sun fitar da sanarwa da ke dauke da kudurin nasu, in da wani yankin sanarwar ke kira ga shugaba Muhammadu Buhari da ya gaggauta aika kudirin doka ga Majalisar Dokoki ta kasa don yin kwaskwarima ga Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel