Da dumi-dumi: Shugaban majalisar dattawa ya dakatar da zaman zauren na kwanaki bakwai, ya bayar da dalilin

Da dumi-dumi: Shugaban majalisar dattawa ya dakatar da zaman zauren na kwanaki bakwai, ya bayar da dalilin

- Tsawon mako guda, ba za a gudanar da zama a majalisar dattijai ba

- Shugaban majalisar dattijan, Ahmad Lawan, ya ce ‘yan majalisar za su mayar da hankali kan sake duba kundin tsarin mulki

- Lawan ya sanar da hakan ne a zauren majalisar na ranar Laraba, 19 ga Mayu

Shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan, a ranar Laraba, 19 ga watan Mayu, ya ba da sanarwar dakatar da zaman majalisar na tsawon kwanaki bakwai masu zuwa.

Da yake magana a ranar Laraba a majalisar dattijan, Lawan ya bayyana cewa makon za a sadaukar da shi ne don sauraren taron yanki kan nazarin kundin tsarin mulki na 1999, jaridun Vanguard da The Nation suka ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Tsohon Babban Alkalin Jigawa Ringim ya mutu a hatsarin mota

Da dumi-dumi: Shugaban majalisar dattawa ya dakatar da zaman zauren na kwanaki bakwai, ya bayar da dalilin
Da dumi-dumi: Shugaban majalisar dattawa ya dakatar da zaman zauren na kwanaki bakwai, ya bayar da dalilin Hoto: @DrAhmadLawan
Asali: Facebook

Shugaban Majalisar Dattawan ya ce:

"Za mu dukufa ga aikin sake duba kundin tsarin mulki a makon gaba daya."

A cewar jaridar Punch, Lawan wanda ya bayyana cewa za a gudanar da zaman a cibiyoyi 12 a duk fadin kasar a ranar Laraba, 26 ga watan Mayu da kuma Alhamis, 27 ga watan Mayu, ya bukaci ‘yan Najeriya da su tabbatar da shiga cikin shirin sosai domin majalisar kasa za ta kasance a bude ga shawarwari masu amfani.

KU KARANTA KUMA: Kyakkyawan hoton tsohon Masallaci a Legas ya haifar da cece-kuce a kafafen sada zumunta

A wani labarin, yan majalisar dattijai sun yi bayani game da wasiƙar da shugaba Buhari ya aike musu a zaman su na jiya Talata.

A wasiƙar da shugaban ya aike musu ya nemi sahalewar su ya karɓo rancen kuɗi kimanin Naira 2.3 tiriliyan don cike gurbin kasafin kuɗi na wannan shekarar.

Bayan karanta wannan wasiƙa a zauren majalisar jiya Talata, labarin rancen ya karaɗe ko ina kafafaen sada zumunta, inda wasu yan Najeriya suka fara sukar shugaban.

Amma shugaban masu rinjaye na majalisar dattijan Najeriya, Sanata Yahaya Abdullahi, yayi ƙarin haske kan wasikar a wata hira da yayi da BBC ta wayar salula.

Asali: Legit.ng

Online view pixel