Wata kungiyar jama’a ta caccaki MURIC, ta ce Musulmi ba zai gaji Buhari ba

Wata kungiyar jama’a ta caccaki MURIC, ta ce Musulmi ba zai gaji Buhari ba

- Wata kungiya mai suna Nigeria Equity Group (NEG) ta caccaki kungiyar MURIC a kan cewa da tayi ba zai yiwu a baiwa Bayarabe tikitin takarar shugaban kasa ba idan ba Musulmi bane

- Kungiyar NEG ta ce tunda Shugaban kasar Najeriya na yanzu, Muhammadu Buhari Musulmi ne, adalci shine a mika mulki ga dan kudu wanda yake Kirista

- Ta ce zai sabawa dokar adalci, daidaito da gaskiya, idan har wani Musulmi ya gaji Shugaba Buhari a 2023

Wata kungiyar farar hula a Najeriya (NEG), ta yi tir da kiran da Kungiyar Kare Hakkokin Musulmi (MURIC) ta yi kwanan nan na neman Bayarabe Musulmi ya gaji Shugaba Muhammadu Buhari a 2023.

MURIC ta yi ikirarin cewa Kiristocin Yarabawa uku sun “mamaye Aso Rock villa”, amma babu wani Bayarabe Musulmi da ya rike mukamin shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa tun bayan samun ‘yancin kai.

KU KARANTA KUMA: INEC ta koka, ta ce babban zaben 2023 na iya samun matsala

Wata kungiyar jama’a ta caccaki MURIC, ta ce Musulmi ba zai gaji Buhari ba
Wata kungiyar jama’a ta caccaki MURIC, ta ce Musulmi ba zai gaji Buhari ba Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

Amma Emeka Nwosu, jagoran kungiyar NEG, a cikin wata sanarwa, ya ce matsayin MURIC ya saba wa ka'idojin mulkin karba-karba don tabbatar da daidaito da adalci a harkar siyasa.

Kungiyar ta lura cewa tun da shugaban kasar na yanzu Musulmi ne daga arewa, adalci shine shugaban kasa na gaba ya zama Kirista daga kudu, jaridar The Cable ta ruwaito.

"Mun lura da kiran da kungiyar Kare Hakkin Musulmi (MURIC), ta yi na neman wani Bayarabe Musulmi ya gaji Shugaba Muhammadu Buhari a 2023," in ji sanarwar.

“Duk da yake Kungiyar Hadin Kan Najeriya (NEG) ta yaba da damuwar masanin Farfesan da MURIC, kan bukatar daidaito, gaskiya da adalci a cikin harkar siyasa ga dukkan kungiyoyi, lamarin 2023 ya wuce abin da Kudu maso Yamma kadai ke iya yanke shawara a kai.

“Yana iya zama muhimmin abu a bayyana a nan cewa kungiyoyin siyasa sun gabatar da tsarin shugabancin karba-karba tsakanin Arewa da Kudancin kasar don magance rashin daidaito a harkokin siyasa tsakanin kungiyoyi daban-daban a kasar, wadanda suka hada da kabilanci da addini.

“Duba ga cewa Shugaban kasa na yanzu Musulmi ne kuma daga Arewa, adalci da daidaito na bukatar cewa shugaban kasar da zai zo na gaba ya zama Kirista daga Kudu.

“Matsayin NEG shi ne cewa zai sabawa dokar adalci, daidaito da gaskiya, wani Musulmi ya gaji Shugaba Muhammadu Buhari a 2023.

KU KARANTA KUMA: Gwamnonin PDP: Muna Son Buhari Ya Amince da Yiwa Kundin Tsarin Mulki Kwaskwarima

"Don kara jaddadawa, muna sake jaddada cewa hanya daya tilo da za ta tabbatar da dawwamammen zaman lafiya, ci gaba da kwanciyar hankali a Najeriya shi ne Shugaban kasar da zai zo ya zama Kirista daga Kudu."

A baya mun ji cewa kungiyar kare hakkin Musulmai watau MURIC ta bayyana cewa ba zai yiwu a baiwa wani dan kabilan Yoruba tikitin takarar shugaban kasa ba idan ba Musulmi bane.

A jawabin da shugaban kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola, ya sake ranar Litinin, ya bayyana cewa tsohon shugaba Obasanjo na kokarin shigo da shugaban bankin cigaban Afrika, Akinwumi Adesina, cikin takarar kujeran shugaba a 2023.

A cewarsa, kokarin sanya Adesina wanda Bayarabe Kirista ne cikin takaran rashin adalci ne da daidaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng