Gwamnonin PDP: Muna Son Buhari Ya Amince da Yiwa Kundin Tsarin Mulki Kwaskwarima

Gwamnonin PDP: Muna Son Buhari Ya Amince da Yiwa Kundin Tsarin Mulki Kwaskwarima

- Gwamnonin jam'iyyar PDP sun bukaci shugaba Buhari ya amince da kwaskwarima ga kundin tsarin mulki

- Sai dai, kwaskwarimar da suke bukata ita ce za ta kara bai wa jihohi karin karfin ikon gudnarwa

- Sun kuma yi kira ga shugaban kasa da ya gaggauta kiran taron majalisar 'yan sanda don bullo da hanyoyin magance tsaro

Gwamnonin jam’iyyar PDP sun yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya aika da kudirin zartarwa ga majalisun dokokin kasa don yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulki ta yadda za a yi karin iko ga jihohi.

Kungiyar gwamnonin na PDP sun yi taro a Ibadan, babban birnin jihar Oyo a ranar Litinin don tattaunawa kan halin da kasa ke ciki, matsalar rashin tsaro, da tattalin arziki, The Cable ta ruwaito.

KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: EFCC Ta Kwamushe Tsohon Gwamnan Kwara da Zargin Karkatar da Kudi

Gwamnonin PDP: Muna Bukatar Buhari Ya Kara Mana Karfin Iko
Gwamnonin PDP: Muna Bukatar Buhari Ya Kara Mana Karfin Iko Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

A karshen taron, sun fitar da sanarwa da ke dauke da kudurin nasu, in da wani yankin sanarwar ke kira ga shugaba Muhammadu Buhari da ya "gaggauta aika kudirin doka ga Majalisar Dokoki ta kasa don yin kwaskwarima ga Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.

Sun bayyana bukatar kwaskwarimar ne saboda neman "karin iko ga jihohi game da tsare-tsaren tsaro da ke karewa ta wata hanyar 'Yan Sanda na Jiha da kuma tsare-tsaren tsaro na gaba daya.

Hakazalika taron ya yi kira ga shugaban kasa da ya kira taron Majalisar 'Yan Sanda nan take don bullo da sabbin dabarun yaki da barazanar da ake fuskanta.

KU KARANTA: Ku Tursasa 'Yan Boko Haram Su Mika Wuya, CDS Ga Kungiyoyin Kare Hakkin Dan Adam

A wani labarin, Gwamnonin jihohi 13 a karkashin jam'iyyar PDP, a yanzu haka suna ganawa a Cibiyar Taron Kasa da Kasa na Cibiyar Kula da Noma ta IITA dake Ibadan ranar Litinin, Daily Nigerian ta ruwaito.

Gwamnonin su ne: Aminu Tambuwal na jihar Sakkwato; Samuel Ortom na Benue; Douye Diri na Bayelsa; Okezie Ikpeazu na Abia da Emmanuel Udom na Akwa Ibom.

Sauran sune: Ifeanyi Okowa na Delta, Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu, Umar Fintiri na Adamawa; Bala Mohammed na jihar Bauchi, Nyesom Wike na Ribas da Godwin Obaseki na Edo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel