Babbar Magana: Zama Gwamna Ƙara Talautad Dani Yayi, Inji Tsohon Gwamna

Babbar Magana: Zama Gwamna Ƙara Talautad Dani Yayi, Inji Tsohon Gwamna

- Tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha, yace zaman shi gwamna na shekara takwas ƙara talautad dashi yayi

- Sanatan wanda yake wakiltar Imo ta yamma ya faɗi haka ne yayin da yake musanta zargin da ake masa cewa ya mallaki kadarori a Abuja

- Okorocha yace shi bai san wata kadara da ya mallaka a Abuja ba, amma gwamnatin Imo ta shigar dashi ƙara

Tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha, ya bayyana cewa ya ƙara talaucewa ne bayan ya jagoranci jihar Imo na shekara takwas,.kamar yadda Punch ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Babu Makawa Sai Mun Hana Fulani Makiyaya Kiwo a Yankin Mu, Inji Gwamnan PDP

Sanatan wanda yake wakiltar mazaɓar Imo ta yamma a majalisar dattijai, ya faɗi haka ne lokacin da yake musanta zargin ya mallaki wasu kadarori da kuɗin gwamnati.

Babbar Magana: Zama Gwamna Ƙara Talautad Dani Yayi, Inji Tsohon Gwamna
Babbar Magana: Zama Gwamna Ƙara Talautad Dani Yayi, Inji Tsohon Gwamna Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Yace: "Na ƙalubalanci kowane mutum yazo da hujjar da zata nuna na mallaki wata kadara da kuɗin gwamnati."

"Ina tunanin mutane sun manta waye Rochas kafin ya zama gwamnan jihar Imo, ina tsammanin sun manta kwata-kwata."

"Idan har akwai abinda zama gwamna ya tsinana mun to shine na ƙara talaucewa fiye da yadda nike a baya. Bansan wata kadara dana mallaka ba a Abuja, ban mallaki komai ba."

KARANTA ANAN: Kotu Ta Yankewa Musulmi 29 Hukuncin Kisa Saboda Rikici Kan Limancin Sallar Idi

Yayin da yake ƙarin haske kan abinda ya faru dashi bayan ya amsa gayyatar hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC), Okorocha yace:

"Na cewa EFCC ba wai nazo bane don amsa kiran da suka yi mun saboda an riga an shigar dani ƙara a kotu, kuma matuƙar ankai ƙara kotu, to babu dama wani yayi katsalandan a cikin lamarin."

"Gwamnatin jihar Imo ta shigar da ƙarata a gaban kotu, kuma muna shari'ar ne a babbar kotun tarayya dake babban birnin tarayya Abuja."

"EFCC na gudanar da aikinsu ne yadda ya rataya a wuyansu, domin inda basu sami wani rahoto ba da ba zasu tsoma baki a cikin lamarin ba. EFCC na aike ne bisa wani ƙorafi da wani mutum ya rubuta musu."

A wani.labarin kuma Kamfanin Wutar Lantarki Ya Katse Duka Layukan Wutar Jihar Kaduna

Kamfanin wutar lantarki na jihar Kaduna TCN, ya katse duka layukan rarraba wutar lantarkin dake jihar domin bin umarnin ƙungiyar ƙwadugo.

Kamfanin yace ya zama waji ya yanke wutar kasan cewar dukkan ma'aikatansa na ƙarƙashin kungiyar ta NLC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262