Rashin tsaro: Gwamnan Arewa ya bayyana mutanen da ke da hannu a sace-sacen mutane da fashi da makami
- Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya yi magana a kan wadanda ke da hannu a aikata laifuka a arewa
- A cewar Mohammed, Musulmai ne ke da alhakin fashi da makami, satar mutane, da sauran laifuka masu nasaba da hakan
- Gwamnan ya kuma gargadi wadanda ke neman a wargaza Najeriya, yana mai cewa ya kamata su guji hakan
A tsaka da yanayin rashin tsaro a kasar, Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya gano mutanen da ke da hannu a matsalolin tsaro a fadin arewa.
Jaridar Sun News ta ba da rahoton cewa Mohammed ya yi ikirarin cewa yawancin ayyukan ta'addanci na baya-bayan nan kamar su satar mutane, fashi da makami, da sauran su Musulmai ne ke ci gaba da aiwatar da su.
KU KARANTA KUMA: Rashin tsaro: Daga karshe Gwamnan Najeriya ya magantu, yace ya san inda yan fashi ke da zama
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 13 ga watan Mayu, yayin da yake zantawa da manema labarai a masaukin shugaban kasa, Ramat House, Bauchi.
Yayin da yake nuna nadama kan yadda mabiya addinin Musulunci ke da alhakin aikata laifi, Mohammed ya lura cewa ba abu ba ne da addini ya yarda da shi.
KU KARANTA KUMA: IBB yana nan da ransa cikin koshin lafiya, majiyoyi sun karyata rade-radin mutuwar tsohon Shugaban Najeriyan
A cewarsa, ya kamata Musulmi su ji tsoron Allah kada su ba addininsu suna mara kyau.
Ya yarda cewa rashin tsaro na ta'azzara daga arewa zuwa wasu sassan kasar, yayin da kuma yake ikirarin cewa ya san inda wadanda ake zargin suke zama, PM News ta ruwaito.
Gwamnan ya kuma gargadi wadanda ke neman ballewar kasar da su daina. Ya yi gargadin cewa duk wani yunkuri na wargaza Najeriya zai haifar da babbar matsalar agaji.
A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Juma'a, ya karbi bakuncin dan marigayi Idris Deby, Mahamat Kaka Deby, wanda shine mukaddashin shugaban kasar Tchad.
Janar Mahamat ya dira fadar Aso Villa ne misalin karfe 11:11 na safe, rahoton TheNation.
Duk da cewa ba'a san abinda suke tattaunawa ba a yanzu, ana kyautata zaton yana da alaka da matsalar tsaro na yan ta'addan Boko Haram a yankin Sahel.
Asali: Legit.ng