IBB yana nan da ransa cikin koshin lafiya, majiyoyi sun karyata rade-radin mutuwar tsohon Shugaban Najeriyan
- Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Ibrahim Babangida bai mutu ba
- An rahoto cewa IBB ya mutu ne bayan ya idar da Sallar Idi a ranar Alhamis 13 ga watan Mayu
- Amma wata majiya, ta ce tsohon shugaban yana ta karbar baki a gidansa na Minna tun ranar Alhamis, 13 ga Mayu
Duk da jita-jitar mutuwar tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), majiyoyi sun ce tsohon shugaban na nan da ransa kuma yana cikin koshin lafiya.
Jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito cewa IBB ya ci gaba da tarbar manyan ‘yan kasa na nesa da na kusa a matsayin maziyartan bikin Eid-el-Fitr a ranar Alhamis, 14 ga watan Mayu, a gidansa na Uphill a Minna, babban birnin jihar Neja.
KU KARANTA KUMA: Jarumi Lawan Ahmad ya zabgawa jaruma mai tasowa mugun mari a wurin shirya fim
Legit.ng ta tattaro cewa jaridar ta ce wata majiya ta kusa da IBB ta lura cewa wasu fitattun ‘yan Neja karkashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Ahmed Mohammed Ketso, sun kai masa (IBB) ziyarar Sallah har yamma.
Rahoton ya kuma jaddada cewa wata majiya tabbatacciya wacce ba za ta so a ambaci sunanta ba ta ce har yanzu Janar Babangida na karbar baki.
Ya ce:
“IBB yana cikin yanayi mai kyau. Baba yana cikin koshin lafiya da nutsuwa.”
Jaridar New Telegraph ta kuma ruwaito cewa wata majiya ta kusa da ahlin, yayin da take karyata rahoton cewa tsohon shugaban sojan da aka haifa a Neja ya rasu a ranar Alhamis bayan Sallar idi, ya ce wasu fitattun ‘yan Neja sun kai masa ziyarar Sallah har zuwa yammacin wannan rana.
Majiyar ta bayyana:
“Yana cikin yanayi mai kyau. Kamar yadda nake magana da ku yanzu, Baba yana cikin koshin lafiya da karfin zuciya. A ranar Alhamis, ya tarbi Janar Abubakar Abdulsalami mataimakin gwamna, Ahmed Muhamad Ketso, Sakataren Gwamnatin Jiha (SSG) Ahmed Matane da sauran mutane da yawa a cikin gidansa na Uphill Mansion.
KU KARANTA KUMA: 'Yan Najeriya ne ke ta rokona in fito takarar shugabancin kasa, Yahaya Bello
“Ya sanya babbar-riga launin ruwan kasa, ya ci abincin rana tare da baƙinsa, kuma dukansu sun yi salla tare. A musulinci, mutuwa ba abune da zamu boye ba. Idan Allah ya ce lokaci ya yi, Janar Babangida zai amsa kiran, ba zai zama jita-jita ba."
A wani labari, Janar Mahamat ya dira fadar Aso Villa ne misalin karfe 11:11 na safe, rahoton TheNation.
Duk da cewa ba'a san abinda suke tattaunawa ba a yanzu, ana kyautata zaton yana da alaka da matsalar tsaro na yan ta'addan Boko Haram a yankin Sahel.
Mahamat Deby ya gaji mahaifinsa ne wanda yan tawaye kasar Chadi suka hallaka a filin daga.
Asali: Legit.ng