Rashin tsaro: Daga karshe Gwamnan Najeriya ya magantu, yace ya san inda yan fashi ke da zama

Rashin tsaro: Daga karshe Gwamnan Najeriya ya magantu, yace ya san inda yan fashi ke da zama

- Gwamna Bala Mohammed ya bukaci ‘yan Najeriya da su marawa gwamnati baya a yakin da take yi da rashin tsaro a kasar

- Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 13 ga watan Mayu, a garin Bauchi, babban birnin jihar

- A cewarsa, wasu mutane da ke da kima a cikin al'umma suna tallafawa 'yan ta'adda

Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya bayyana cewa ya san inda 'yan fashi da ke addabar kasar nan suke da zama.

Jaridar PM News ta bada rahoton cewa ya yi kira ga jihohi da kananan hukumomi da su hada hannu da gwamnatin tarayya wajen magance matsalolin tsaro a Najeriya.

KU KARANTA KUMA: IBB yana nan da ransa cikin koshin lafiya, majiyoyi sun karyata rade-radin mutuwar tsohon Shugaban Najeriyan

Rashin tsaro: Daga karshe Gwamnan Najeriya ya magantu, yace ya san inda yan fashi ke da zama
Rashin tsaro: Daga karshe Gwamnan Najeriya ya magantu, yace ya san inda yan fashi ke da zama Hoto: @SenBalaMohammed
Asali: Twitter

Legit.ng ta tattaro cewa Mohammed, wanda ya bayyana hakan a Bauchi a ranar Alhamis, 13 ga watan Mayu, ya ce gwamnatin tarayya ba za ta iya magance matsalolin ita kadai ba.

Ya ce:

"Hakkin gwamnatin tarayya ne, da na jihohi da na kananan hukumomi, gami da dukkanin cibiyoyin gargajiya a kasar nan. Wadannan matsalolin za a iya magance su ne ta hanyar hada karfi da karfe da hadin kai daga gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi.

KU KARANTA KUMA: Na Allah basu karewa: Dan sanda ya mayar da N1.2m da ya tsinta wurin hatsari a Kano

"A matsayinmu na kasa, muna fuskantar kalubale ta fuskoki da dama na aikata laifuka, aikata laifi da ta’addanci. Dole ne mu kasance masu karfin gwiwa mu fadi hakan kuma wannan ba wani abu ba ne da za a yarda da shi a cikin addinin Musulunci."

Jaridar The Nation ta kuma ruwaito cewa gwamnan ya yi ikirarin cewa wasu mutane ne ke taimaka wa 'yan ta'addan, yana mai cewa ya kamata a tsamo su.

Mohammed, wanda ya ce Najeriya ta kasance a dunkule kuma a hade, ya kara da cewa za a cimma manufa ta hanyar fahimtar juna.

A wani labarin, gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong, yace tsohon shugaban ma'aikatan tsaro, janar Joshua Nimyel Dogonyaro, kafin rasuwar shi ya bashi shawara kan yadda za a shawo kan matsalar rashin tsaro a jihar.

Ya kara da cewa marigayin janar din yayi babban kokari wurin baiwa kasar Najeriya kariya, Daily Trust ta ruwaito.

Lalong, wanda ya ziyarci iyalin marigayin domin ta'aziyya a Rayfield Jos, ya ce marigayi Dogonyaro ya nuna hazakarsa ta yadda ya bautawa kasar nan a yayin da yake aikinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel