Wata Mata Ta Gina Muhallin da Zai Ke Tsawaita Rayuwar Dan Adam a Duniya
- Wata mata ta dauki gwagwarmayar gyara muhallin ta zuwa kyakkyawan yanayi mai daukar hankalin gaske
- Ta gina wani muhallin mai mazaunai bakwai wanda ake ganin za su taimakawa mutane su tsawaita rayuwarsu a doron kasa
- Muhallin na da wasu kyawawan yanayi na musamman wadanda suka hada da kududdufin kifi, dakunan taro da sauransu
Wata mata ta samu nasarar farko a kasar Togo a Afirka tare da samar da yanayin muhalli mai kyau wanda ta yiwa lakabi da ecovillage.
Wata mai fafutukar kare muhalli da aka ambata da suna Tokunbo Ige ta bayyana a shafin LinkedIn don nuna mazaunin da ta gina, wanda a cewarta, tana da nufin taimakawa ne wajen tsawaita rayuwa ta hanyar samar da rayuwa mai kyau.
KU KARANTA: Karamar Sallah: An Jibge 'Yan Sanda 3200 a Imo Don Tabbatar da Tsaro
Kyakkyawan muhallin mai mazaunai bakwai ya na kunshe da kududdufin kifi, tafkin wanka, dakunan taro guda biyu, gidan cin abinci da dai sauran abubuwan jan hankali masu ban sha'awa ga manya da kuma yara.
Ige wacce ta bayyana ecovillage a matsayin gudunmawarta ga kulle-kullen annobar Korona ta ce an gina muhallin ne don kiyaye lafiyar muhalli.
Kamar yadda sunan ya nuna kuma daga hotunan da ta bayyana, ginin an tsara shi na musamman ne don rage abubuwan da ke gurbata mahalli da kuma samar da wutar lantarki da kansa.
Mutane a shafukan sada zumunta sun yaba da wannan aiki kamar yadda suka ga abin ya burgesu.
Wonuola Coker ya ce: "
Ya yi kyau sosai. Kin yi kokari 'yar uwa! Ina taya ki murna. Ina fatan ya ci gaba da girma da daukaka da sunan Yesu."
Angelle B. Kwqemo ya rubuta:
"Karamar aljanna. Aikin kauna. Ina taya ki murna."
KU KARANTA: Yan Sanda Sun Gargadi 'Yan Siyasar Kwara Kan Taron Siyasa a Filin Sallar Idi
A wani labarin daban, Gwamnatin Tarayya a ranar Talata ta amince da daya daga cikin bukatun ma'aikatan kiwon lafiya ta hanyar tsawaita shekarun ritaya zuwa shekaru 65.
Gwamnatin ta kuma amince da shekaru 70 a matsayin shekarun ritaya ga kwararrun likitoci, Daily Trust ta ruwaito.
Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige, ya bayyana hakan ne a Abuja bayan ganawa tsakanin kwamitin Shugaban kasa kan albashi, da Kungiyoyin Kwararru na fannin Kiwon Lafiya da Kungiyoyin Kwadago kan batun Alawus na Hadari da kuma shekarun ritaya.
Asali: Legit.ng